✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Oba na Benin ya karrama shugabannin Arewa

A karshen makon da ya gabata ne majalisar Oba na Benin ta karrama wasu fitattun mutane, domin gogewarsu ko kwarewa da iya zama da jama’a…

A karshen makon da ya gabata ne majalisar Oba na Benin ta karrama wasu fitattun mutane, domin gogewarsu ko kwarewa da iya zama da jama’a da gaskiya da rikon amana, ciki kuwa har da Shugaban Al’ummar Arewa Mazauna Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh; wanda ya samu takardar shaidar karramawar da a tarihin zaman al’ummar Arewa shekaru aru-aru a Jihar Edo, babu wani daya da  ya taba samun irinta a fadar ta Oba, duk da irin dangantaka ta mutunci da ke tsakanin masarautar da shugabannin al’ummar Arewa.
A madadin Oban na Benin, shugaban majalisar masarautar, Cif Obasogie ne ya mike ya yi irin gaisuwar girmamawa ga fadar Oba, sannan ya mika wa wadanda aka karrama din takardar shaidarsu.
Bayan kammala taron, wakilinmu zanta da Alhaji Badamasi, inda ya fara bayaninsa da godiyar Allah kuma ya gode wa Oba da ’yan majalisarsa cikin ladabi. Daga nan kuma sai ya ci gaba da bayyana farin ciki da bayar da shawarwari na ganin an dore da ci gaba da zaman lafiya tsakanin juna na kowane bangare.
“Da farko mun gode wa Allah da Ya yi mu kuma Ya sa irin wannan tunani a zuciyar wadannan shugabanni har suka yi wani bincike, domin gano cancantar kowa da matsayinsa kuma Allah cikin ikonSa ya sa suka gano cewa mu din nan muna iya kokari a kan ganin mun samar da dorewar zaman lafiya, ba a nan jihar kadai ba har da kasarmu Najeriya baki daya. Don haka na kara godiya ga Allah.”
Ya ja hankalin al’ummar Arewa mazauna jihar da sauran jihohin kudu baki daya a kan su gyara halayyarsu. “Ina shawartar jama’armu da su kasance masu rikon amana da tsoron Allah tare da kwatanta gaskiya a kodayaushe, su kuma rika kusantar sarakunan gargajiya na nan kudu da kuma ainihin sarakunanmu da sauran shugabanni; su rika yi wa mabiyyansu adalci da gaskiya. Wannan zai kara musu martaba.” Inji shi.