✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadana sai wata rana

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Tun kamar wata uku da suka wuce musulmin duniya gaba daya hankalinmu ya karkata ga isowar wannan wata…

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai.

Tun kamar wata uku da suka wuce musulmin duniya gaba daya hankalinmu ya karkata ga isowar wannan wata mai alfarma da nake shirin yi wa bankwana a halin yanzu. Mun kasance dukanmu muna masu addu’a da daukin cewa ’Ya Allah Ka nuna muna isowar wannan wata na Ramadana’’ To cikin ikon Allah ga mu tsundum a cikinsa, alamar da ke nuna cewa kafin gobe kuma, za ka ji an fara fadin yau saura wata biyu a fara azumin gari duka (Ramadan). To sai dai kuma, shin muna tafiyar da wannan wata mai alfarma kamar yadda ya dace a tafiyar da shi? Ko kuma muna nan mun saki baki muna jiran sai wata shekara idan ya sake dawowa?
Ya ‘yan’uwa musulmi, muji tsoron Allah! Mu sani watan Ramadana rahama ne da jinkai ga wannan al’umma, saboda haka ya zama wajibi akanmu, mu kiyaye hakkokinsa. Daga cikin wadannan hakkokin kuwa harda kame harshenmu daga ambaton dukkan wani mutum da sharri, mu kame harshenmu daga miyagun kalamai, kalamai na Allah wadai marasa amfani. Ya ishi mutum hasara ya saki harshensa yana ta fadar duk abin da yake son fada ba tare da la’akari da amfani ko rashin amfanin abinda yake cewar ba. Irin wannan hali yakan sanya mutum cikin wadanda suka yi hasara maimakon cin riba a wannan wata.
Ya ku bayin Allah, mu tuna da zancen manzo SAW a inda yake cewa: ‘’ Duk wanda watan Ramadana ya shigo bai yi wani abu da Allah zai gafarta mashi ba, Allah Ya nisanta shi ga rahama.’’ Ashe ko maimakon mu saki baki zuwa surutu, ya fi dacewa ne mu juyar da harshenmu zuwa ga ambaton Allah, neman gafara da horo da aikata khairi. Kwana ashirin da tara ne ko talatin kacal, idan mun kasa kame kanmu a wannan wata, ashe ba mu san yadda za mu tafiyar da sauran watanni 11 na bayan Ramadana ba.
Ya ku ‘yan’uwana na jini da na musulunci, ku zo mu gudu tare mu tsira tare! Addu’ar manzon Allah karvavviya ce. Kuma babu shakka, ba karamar hasara ba ce, ace irin wannan wata ya shigo mutum bai samu kusanta ga Allah ba. To har yaushe muke shirin samun kusanta a gurin Allah idan mun kasa samu a wannan wata? Zuciyoyinmu suna yaudararmu ta hanyar nuna muna cewa akwai sauran lokaci. Da yawa daga cikinmu akwai masu tunanin cewa su jira sai kwanakin goman karshen wata sannan su kame kansu ko su dage ga ibada, wannan wani salon yaudara ne da zukatanmu suke riya muna. Duk abinda ya hana mu maida hankali a yanzu, shi ne abinda zai hana mu maida hankali idan wannan kwanakin karshen suka zo.
Ya zama wajibi mu zare damtse ta hanyar ziyartar wuraren da ake karatun Alkur’ani (Tafsiri) domin muji sakon Allah mai girma da ya aiko muna. Mu rika salloli na nafila, mu yawaita karatun Alkur’ani da bayarda sadaka. Mu sadar da zumunta mu tausayawa mai rauni. Mu kiyaye fa, bara wasu da su aka yi Ramadan, amma a wannan shekara an dawo ba dasu ba! Muma babu shakka za a zo wani watan ba tare da mu ba, hasalima babu mai tabbacin wannan ba shi ne watan Ramadan na karshe a rayuwarmu ba.
Muna rokon Allah Ya arzittamu da alkhairukan wannan wata, Allah Ka sa muna cikin wadanda za su kuvuta daga shiga wuta, Allah Ka sa wannan wata ya zama jinkai da rahama garemu, Allah Ka sa ya zama sanadiyar haduwar kawunan musulmi baki daya. ‘Yan’uwa sai mun sake haduwa da ku a cikin wani rubutu na daban, kai kuma RAMADANA SAI WATARANA.

Nasir Abbas Babi
08033186727.