✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin fahimtar Hadisi ake haihuwar ‘ya’yan da ba a iya kula da su – Hakimi

Hakimin Unguwar Shanu kuma Falakin Zazzau Alhaji Ibrahim Abba-Kura ya ce rashin fahimtar Hadisin Manzon Allah (SAW) a kan haihuwa ne ya jifa wasu ’yan…

Hakimin Unguwar Shanu kuma Falakin Zazzau Alhaji Ibrahim Abba-Kura ya ce rashin fahimtar Hadisin Manzon Allah (SAW) a kan haihuwa ne ya jifa wasu ’yan Arewa cikin matsala game da haihuwar ’ya’ya, inda wasu ’yan Arewa Musulmi ke haihuwar ’ya’ya masu yawa da ba za su iya daukar nauyi ko tarbiyyantar da su ba.

Hakimin ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a gidansa, inda ya ce wasu iyaye sukan nuna halin ko-in-kula ga ’ya’yansu, ba su damu da cinsu, ko suturarsu ba balle wurin kwana, kuma hakan ne ke jifa ’ya’yan su zama ’yan daba ko masu shaye-shayen kwayoyi.
“Mutane suna yi wa Hadisin Manzon Allah (SAW) na cewa “Ku yi aure ku hayayyafa, domin in yi alfahari da yawanku ranar tashin Alkiyama.” Mummunar fassara. Irin wadanan bata-garin ’ya’yan ne Manzon Allah (SAW) zai yi alfahari da su a Ranar Alkiyama? Wannan rashin fahimtar ainihin abin da Annabi (SAW) yake nufi da wannan Hadisi ne ya jifa wasu al’ummar Arewa cikin matsala. Yanzu ga yara nan babu tarbiyya saboda wasu iyayen ba su iya daukar nauyi ko tarbiyyantar da ’ya’yan da suka haifa,” Hakimin sai ya yi kira ga iyaye su sanya ido a kan ’ya’yansu wajen ganin sun samu tarbiyya tagari domin Allah da Ya ba su amanar ’ya’yan zai tambiye su yadda suka kula da su a Ranar kiyama.
Ya bukaci iyaye su tabbatar ’ya’yansu na zuwa makaranta, kuma su rika sanya ido a kan irin abokan da suke yawo da su da sauran abubuwan da za su taimaka wajen sanya yaran a kan turba tagari.
Game da matakin da suka dauka wajen kawo karshen miyagun ayyukan matasa masu shaye-shaye a Unguwar Shanu, ya ce kafa kwamitocin tsaro a unguwannin da ke gundumarsa ya yi matukar taimakawa.
“Wannan kwamiti na tsaro yana da wakilcin akalla mutum biyu daga kowace unguwa, kuma akasarinsu mutane ne da suka yi fice, kuma masu kishin ci gaban jama’arsu. Kuma kwamitin ya samar da wasu zaratan matasa da suke bayar da gudunmawa a harkar tsaro, tare da goyon bayan masu unguwanni da ’yan banga da sauransu,” inji shi.
Falakin na Zazzau ya bukaci gwamnatin jihar da ta rika tuntubar shugabannin al’umma kamar sarakuna da hakimai yayin daukar wasu matakai da suka shafi jama’a.