✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rigima kan katin memorin waya ya haddasa mutuwar mutum biyu a Bauchi

Fada tsakanin ’yan uwa kan katin memori na waya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a Unguwar Makera da ke karamar Hukumar Toro a Jihar…

Fada tsakanin ’yan uwa kan katin memori na waya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a Unguwar Makera da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti ya tabbatar da aukuwar al’amarin. Ya ce bisa bayanin da suke da shi kan al’amarin, rikici ne ya faru tsakanin Haruna Adamu da kuma Isiyaku Abdullahi kan katin memori na waya, inda suna ciki yin fadan sai kannensu biyu suka shiga cikin fadan. Sai iyayensu, baban Ishaku Adamu da kuma mahaifin Haruna Abdullahi su ma suka shiga cikin fadan.

Ya ci gaba da cewa ana cikin fadan sai Abdulkarim Abdullahi ya dauki wuka ya soka wa Haruna Adamu, inda ganin haka sai kanin Haruna mai suna Abubakar Adamu shi ma sai ya dauki adda ya sara wa Isiyaku Abdullahi. A sakamakon haka ne Haruna da Isiyaku dukkansu biyu suka rasu.

Kakakin ya ce bayan da aka dauki bayanan dukkansu, nan take Abdulkarim da Abubakar suka amsa laifinsu na cewa sun kashe Haruna da Isiyaku kuma an tsare su bayan da aka gurfanar da su gaban Kotun Majistare ta biyu da ke Bauchi.

Jami’in ’yan sandan ya roki mutane da su guji daukar doka a hannunsu, su rika hakuri suna kai rahoton dukkan sabanin da ya shiga tsakaninsu ga hukuma, sannan ya jaddada kudirin ’yan sanda na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Wani mazaunin unguwar ya ce wannan al’amari ya tayar masu da hankali kwarai saboda yadda ’yan uwan suka yi fada na dangi a kan katin memori kawai.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan al’amarin, wani malamin addinin Musulunci, Malam Tijjani Kolo ya gargadi al’umma da su guji bin son zuciyarsu har su yi abin da zai kai su ga shiga wuta. “Manzon Allah (saw) ya ce idan Musulmi biyu suka hadu da takubbansu guda biyu, da wanda ya kashe da wanda aka kashe duk suna wuta. Sahabbai suka ce masa ya ma’aikin Allah, wannan wanda ya yi kisa ina ruwan wanda aka kashe kuma? Ya ce shi ma yana kwadayin ya kashe abokinsa ne. Saboda haka akwai hadari wajen kashe rai,” inji shi.

Malamin ya roki iyaye da shugabanni da su rika zama masu yin sulhu da shiga tsakani idan aka samu tashin hankali, maimakon fadawa ciki don a yi fadan da su.