✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruftawar cocin Legas ya ci Mutanen Afirka ta Kudu 67

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Mista Jacob Zuma ya ce kimanin ’yan kasar 67 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka…

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Mista Jacob Zuma ya ce kimanin ’yan kasar 67 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin da ginin wani coci ya rushe a Legas a ranar Juma’ar da ta gabata.Wata sanarwa da Mista Jacob Zuma ya fitar ta ce wannan shi ne hadari mafi muni a tarihi da aka taba samun ‘yan kasar masu yawa sun mutu lokaci guda a wata kasar waje.
Wasu kungiyoyin coci-coci biyar daga Afirka ta Kudu suna ziyara a cocin Synagogue Church of All Nations da ke Legas lokacin da sashin saukar baki na cocin ya ruguje.
Kawo yanzu dai ba a kai ga tantance adadin mutanen da suka mutu a lamarin ba, sai dai hukumomin Najeriya sun ce mutum 62 ne suka mutu a hadarin
A ranar Talata, ma’aikatan agaji sun zakulo wata mace daga baraguzen ginin cocin da ranta amma ta samu raunuka.