✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shan giyar Gogoro ya zama laifi a Najeriya

Sakamakon mutuwar fiye da mutum 60 a Jihar Ribas da wasu kuma a Jihar Ondo da ake zargin sun kwankwadi giyar Gogoro ne, Gwamnatin Tarayya…

Sakamakon mutuwar fiye da mutum 60 a Jihar Ribas da wasu kuma a Jihar Ondo da ake zargin sun kwankwadi giyar Gogoro ne, Gwamnatin Tarayya ta haramta shan giyar a fadin kasar nan.

Gwamnatin ta haramta shan giyar ne a daidai lokacin da aka tabbatar da mutuwar mutum 38 sakamakon shan giyar a Jihar Ribas da kuma wasu a garin Ode-Irele da ke Jihar Ondo, mutuwar da aka dangana ta da shan giyar Gogoro.
Lokacin da yake jawabi ga manema labarai, Darakta Janar na Hukuma Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) Dokta Paul Orhii ya ce “Binciken farko da Cibiyar Kare Yaduwar Cututtuka masu Yaduwa ta kasa (NCDC) da Hukumar Lafiya ta Duniya ya gano cewa babu wata cutar da ake dauka da ta jawo mace-macen, inda suka tabbatar da cewa akwai yiwuwar guba ce ta jawo hakan, kuma suka shawarci Hukumar NAFDAC ta gudanar da wani binciken a kai.
Dokta Orhii ya ce “Alamun cutar da wadanda lamarin ya shafa suke nunawa sun hada da amai da rashin gani sosai da ciwon kai da mutuwar jiki da fita daga hayyaci da kuma mutuwar fuju’a da mutum 18 suka yi.”
Dokta Orhii wanda ke tare da Daraktan Hukumar NCDC Farfesa Abdulrahman Nasidi a lokacin ganawar ya ce dukkan alamu sun nuna cewa, “Wadannan alamu ne na wata guba da ake sha.”
Shugaban na NAFDAC ya kara da cewa, “Sakamakon binciken da suka gudanar a dakuna gwaje-gwajen kimiyya ya nuna an samu samfurin guba guda biyar da suke da alaka da giyar da aka yi daga itatuwa (Gogoro), kuma gubar ta Gogoro tana yi wa jini illar da ta kai milligram 1500 zuwa 2000 wanda ba makawa ta jawo mutuwar majiyancin da bai samu magani ba.”
Shugaban ya ce bisa lura da mugun hadarin da shan giyar Gogoro da ake yi ne ya say a zama wajibi “a gargadi jama’a su kaurace wa shan nau’o’in giyar Gogoro marasa rajista da aka hada a kasar nan da saura masu rajista da suke da daci.”