✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 50 bayan Sardauna da Tafawa balewa:

Har yanzu ba a samu kamarsu ba – danmasanin Kano Aminiya: Yallabai yau shekara 50 ke nana da kashe marigayi firaminista Abubakar Tafawa balewa. A…

Har yanzu ba a samu kamarsu ba – danmasanin Kano

Aminiya: Yallabai yau shekara 50 ke nana da kashe marigayi firaminista Abubakar Tafawa balewa. A matsayinka na ministansa ko za ka bayyana mana yadda aka kashe shi?
dan masani: Duk da cewa ban fiye son yin magana akan wannan lamari ba, amma ba na mantawa wata rana da azumi da daddare ana gobe za a kashe shi (Firaminista) na je gidansa don in gan shi a kan nema wa Alhaji Baba danbaffa takardar izinin jigilar alhazai zuwa Saudiyya wanda aka hana shi saboda wasu dalilai. Sai na iske yana tare da wasu daga cikin ministocinsa da suka hada da Okotie Eboh, don haka ya ce a shaida min ba zai iya ganina a wanann lokaci ba sai washegari. Bayan na koma gida, da misalin karfe 3:30 na dare sai wata yarinya ta kira ni a waya, sai ta ce ita ce kanwar matar odalin Firaminista, ta sanar da ni cewa ga sojoji sun kewaye gidan Firaminista. Nan take na yi salati. Haka na fito daga ni sai rigar barci, babu ko takalmi a kafata. Ga babu direba, don haka sai na dauki keken dana na tafi gidan nasa. Tun daga nesa na hango gida a bude, hakan ya tabbatar min babu lafiya. A nan ma na ji sojojin suna cewa,” waye a nan? Ko wane ne ma ya koma kada ka zo nan. Hakan ya sa na bar wurin na nufi hanyar gida. A kan hanyata ne na shiga gidan makwabcina minista mai kula da sojoji  Ibrahim Tako, Galadiman Bidda, na sa aka taso shi  daga barci na gaya masa halin da ake ciki. A nan ya nemi mu je Barikin Obalande inda muka tambayi sojojin halin da ake ciki, a nan suka gaya mana cewa Ironsi ya zo ya yi musu jawabi game da lamarin, inda ya ce musu wai wasu mutane ne suka so kai wa wasu manyan mutane na farar hula da sojoji hari, amma ya yi kokari ya wargaza shirinsu, amam wai ya gaya musu cewa daga yanzu kada su saurari kowa idan ba shi ba, ko Birgediya Zakariyya Maimalari.  A nan sai na gaya wa Ibrahim Tako cewa ya kamata ya rubuta wa Ironsi takarda don neman karin bayani game da halin da ake ciki. A nan muka samu amsa daga Ironsi cewa a wanann lokaci komai ya daidaita mu kwantar da hankalinmu. Hakan ya sa na koma gida har na samu na kwanta na yi dan barci.
Bayan an yi sallah sai ga yara daga gidan Firaminista suka zo suka gaya min cewa matan gidan sun ce a sanar min cewa a cikin dare wasu sun zo sun tafi da Firaminista. A nan take na yi salati. A nan muka yi kokari mu ministoci daga Arewa muka hadu a gidan mataimakin shugabanmu Minista Zanna Bukar Yarima, kasancewar shugabanmu Minista Alhaji Inuwa Wada ba ya nan, don mu tattauna game da matakin dauka. A nan Jakadan Ingila ya gaya mana cewa mu yi kokari mu nada wakilin firaminista, sannan mu roki Ingila ta ba mu taimako don wargaza wannan tawaye. A nan aka tura ni tare da Shehu Shagari wurin sauran ‘yan uwanmu ministocin Jihar Yamma don mu sanar da su halin da ake ciki, tare da tattaunawa a kan wannan shawara. A nan muka samu Kem Nbaduwe, wanda shi ne shugabansu,  muka gaya masa shawarar da muka yanke. A nan ya gaya mana abin da ya gaya mana. (ba zan fadi abin da ya fadi ba).  Daga nan sai muka nufi gidan Sanata Prince Orizor, wanda ke rikon shugabancin sanatoci, kasancewar a lokacin shugaban Sanatoci Dokta Azikwe ba ya kasar. Muka roke shi don ya yarda a rantsar da Minista Zanna Yarima a matsayin wakilin Firaminista, a nan ma ba mu yi nasara ba. Haka dai muka hakura. (Ba na son na fadi abubuwan da suka faru dalla-dalla, kamar yadda nake fadi kullum zaman lafiya ake kokarin tabbatarwa a kasar, ba ma son rabuwar kai. Mu dai muna addu’ar Allah Ya ji kansa da Rahama)
Daga baya nake jin labari daga wurin Madakin Bauchi, wanda amininsa ne, tare suka yi karatu a Katsina. A lokacin shi ma yana Sanata. Ba na macewa tare da shi muka dauki gawar Firaminista zuwa Bauchi. Madakin shi ya gaya min cewa a lokacin da na zo a daren da za a kashe Firaministan yana magana da ministocin NCNC da suka hada da Okotie Eboh da Kem  Nbaduwe, kan abin da ke faruwa a Jihar Yamma. A nan yake gaya musu cewa shi bai goyi bayan abin da ke faruwa a Jihar Yamma ba na kashe-kashe da ake yi. Don haka a daren ya sanar da su cewa zai sa dokar  ta-baci a Jihar Yamma zai kuma sauke Akintola a matsayinsa na Firimiyan Yamma, zai kuma nada kantoma a madadinsa. A nan ya yi rubuce-rubuce ya bai wa Kem  Nbaduwe ya ce ya tafi da shi gida ya karanta idan da gyare-gyare ya yi da sassafe ya kawo masa, don ya karanta wa jama’ar kasa. Haka kuma a nan take ya dauki waya ya gaya wa Sardauna cewa ga abokinsu (Akintola) ya kai su inda ba za su iya dawowa ba, har ya sanar da shi matakin da ya dauka a kan lamarin.
Maganar da Firaminista bai yi ba ke nan, domin a wannan daren aka dauke shi, watakila ma a daren aka kashe shi. Ina ganin da Firaministan Abubakar Tafawa balewa ya yi wannan maganar tare da sanya dokar ta-baci a Jihar Yamma, to da watakila ya zama silar haihuwar rigima a Jihar Yamman. Akwai wani yaron dan sanda da ke gidan Firaminista mai suna Kaftan, shi yake gaya min cewa a cikin daren da aka dauke Firaministan, Jakadan Ingila ya je gidan Firministan inda ya sanar masa cewa yana da labarin za a yi juyin mulki a yau, don haka ya tashi su tafi gidansa. Amma sai Firaministan ya ki, inda ya shaida amsa cewa a iya saninsa bai yi wani laifin da za a yi masa wani abu ba. Haka Jakadan Ingilan nan ya hakura ya tafi ya bar shi a gidan. Hakan ya tabbatar da cewa mutuwarsa kaddara ce kawai.

Aminiya:Shin gaskiya ne makusantansa ne suka kashe shi?
dan masani: Ban taba jin wannan magana ba. Kai ni ban taba zaton hakan za ta kasance ba, kasancewar shi marigayi Firaminista mutum ne da yake kyautata mu’amalarsa da mutane na kusa da na nesa, ba na zaton wani zai iya aikata hakan gare shi. An ce fa saboda kyawun halinsa a daren da aka zo za a tafi da shi yaran da ke aiki a gidan suka rika bin sojojin suna rokonsu da kada su cutar da shi, suna gaya musu cewa shi Firaministan babu ruwansa da kowa.

Aminiya: Shin kana ganin an samu ci gaban da ya kamata a Najeriya bayan shekara 50 da kashe shi?
dan masani: Ba a samu ba. Najeriya ta fara da shugabanni masu kishin kasa, wadanda ci gaban kasar ne a gabansu ba wai su tara abin duniya ba. Shi ya sa a wancan lokaci suka yi kokarin wajen tafiyar da kasar don ciyar da ita gaba. Saboda halayen Firaminista na kwarai manyan kasashen duniya sun yi ittifaki cewa da za a ce Tafawa balewa da Shugaban Indiya Neru da za su samu shekaru 15 zuwa 20 suna gudanar da shugabancin kasashensu, to kasashensu za su iya yin kunnen doki da kasashen da suka ci gaba, irin su Amurka da Ingila da sauransu.
Abin da ya jawo mana rashin ci gaba a kasar nan shi ne watsi da muka yi da koyarwar da shugabanninmu na baya irin su Firaminista suka yi mana. Batun ci gaba sai dai ko nan gaba, don bai kamata Musulmi ya yanke zato daga samun Rahamar Allah ba. Muna fatan nan gaba mu samu shugabanni masu kishin kasar, masu son talakawa.

Aminiya: Wadanne abubuwa ne na baya za su yi koyi daga marigayi Firaminista?
dan masani: Duk duniya ta yarda cewa Alhaji Abubakar Tafawa balewa dattijo ne, mai amana, mai kishin kasa, mai kamanta gaskiya da adalci a dukanin abin da yake yi. Rayuwarsa gaba daya abar koyi ce ga ‘yan baya. Lokacin da Allah ya karbi ransa ba shi da kwabo a banki, ba shi da gidajen haya, ba shi da gonaki, ba shi da motocin haya, a matsayinsa na Shugaban kasa mai arzikin man fetur, amma bai mallaki rijiyar mai ba. Tun daga shekarar 1955 zuwa 1966 nake ministan man fetur a wancan lokaci amma bai taba neman a bai wa wani lasisin sayar da mai ko a ba shi rijiyar mai ba. Ba na mancewa, akwai lokacin da za a yi bikin ‘ya’yansa, yana ofishinsa a zaune sai wani Bature abokinsa ya same shi ya yi tagumi, ya tambaye shi dalili, a nan Firaministan ya sanar da shi halin da yake ciki, cewa ba shi da kudi. Anan Baturen ya ba shi shawara ya karbi bashi a banki ta yadda za a rika cirewa daga albashinsa, amma sai ya gaya masa cewa abin da yake tsoro shi ne idan ya karbi bashin, to idan su kuma suka nemi wani abu daga gare ni, musamman wanda ba ya bisa ka’ida yaya zan yi da su? Bai karbi bashin ba, sai ya ce Allah Ya buda masa wata hanyar.
Akwai abin kwaikwayo a yanayin siyasarsa, siyasa ce ta ra’ayi, ba ta cin mutunci ba. A wancan lokaci, duk da cewa akwai bambance-bambance na addini da na kabila a tsakaninsu, amma hakan bai sa sun ci mutuncin junnasu ba. Shi ya sa Najeriyar ta samu kima a idon duniya, duk inda dan Najeriya ya je a wancan lokaci da karfinsa yake takawa.  Ina iya tunawa ina dan shekara 29 da haihuwa ya  nada ni minister, shi ya sa ake ganina a matsayin dan gaban goshinsa, saboda ni ne karami, a duk lokacin da aka yi wani taro na ga su Akintola, gwiwa bibiyu nake tsugunawa in gaishe su, duk da cewa ba jam’iyya daya muke ba. Na samu wanann tarbiyya ne daga Firaminista.
A lokacin da aka yi juyin mulki, kasancewar ba gwamnati ce ta tara abin duniya ba, sai da muka yi rancen kudi sannan muka turo wa iyalanmu Arewa.