✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takarar Shugaban kasa: Ana shirin gumurzu a APC

A yayin da shekarar zabe ta 2015 ke kara kawo jiki, ’yan siyasa na ta kara motsa tsimi da kara kaimi a jam’iyyinsu, domin ganin…

A yayin da shekarar zabe ta 2015 ke kara kawo jiki, ’yan siyasa na ta kara motsa tsimi da kara kaimi a jam’iyyinsu, domin ganin sun kai ga gaci. A jam’iyyar APC akwai zaratan ’yan takara guda uku da ke fafutukar ganin sun canke tikitin takarar Shugabancin kasa a karkashinta. Watau, tsohon Shugaban kasa, Janar Muhammad Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da kuma Gwamnan Jihar Kano na yanzu, Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso.

A nasa bangaren, daya daga cikin ’yan takarar da ke neman APC ta tsayar da shi takarar shugabancin Najeriya a badi, Janar Muhammad Buhari, a ranar Larabar da ta gabata ne ya kaddamar da bukatarsa ta tsayawa takarar, a karkashin jam’iyyar APC. Taron ya gudana ne a filin taro na Eagle Skuare, Abuja.
Wannan, shi ne karo na hudu da Buhari ke takara, inda da farko ya fara tsayawa a 2003 a karkashin jam’iyyar ANPP, inda ya kalubalanci tsohon Shugaban kasa, Janar Obasanjo na PDP. A karo na biyu a 2007, ya kalubalanci marigayi Shugaban kasa Umar Musa ’Yar-aduwa. A 2011 kuwa, ya tsaya takara ne a jam’iyyar CPC, inda ya fafata da shugaba mai ci a yanzu, Goodluck Jonathan na PDP.
A taron kaddamar da kansa da ya yi a Abuja, Janar Buhari ya ce ya sake dawowa takara ne da nufin wancakalar da gwamnatin PDP, wacce a cewarsa ta kakaba wa al’umma talauci da rashin tsaro.
“Kusan kowa na rayuwa cikin tsoro da fargaba saboda ta’addancin kungiyar marasa tsoron Allah da ake kira Boko Haram da masu kashe mutane a kauyuka da birane, da ’yan fashi da makami da suka kankane manyan tituna da masu garkuwa da mutane don amsar fansa; wanda haka ya sanya al’umma ke kaura suna barin mazaunansu, suna rayuwa cikin kunci da tsoro.” Inji shi.
A yayin da yake kalubalantar jam’iyya mai mulki, ya ce tun da aka fara mulkin dimokuradiyya a 1999, PDP ce ke mulkin kasar nan kuma ta shigo da tsare-tsare da suka maida kasar nan baya.
“Tun 1999, PDP ke mulkin kasarmu, wanda ya durkusar da ita. A iyaka sanina, ba a taba raba kan ’yan Najeriya ba kamar wannan lokacin kuma duk laifin wannan gwamnati ce marar tunani, marar alkibla, wacce ta takarkare kan mulki don ta ci gaba da sata har abada. Mu a APC, mun kuduri niyyar dakile su, za mu ceto ’yan Najeriya daga kangin PDP.” Inji Buhari.
Haka kuma, Buhari ya koka da yadda rashin wutar lantarki ya durkusar da kamfanoni a kasar nan, musamman kuma da yadda noma da kasuwanci suka tagayyara, wanda haka ya haifar da rashin aikin yi.
Domin dawo da martabar Najeriya, Buhari ya yi alkawarin kawo gyara, inda ya shirya muhimman al’amura guda tara da zai amfani da su wajen kawo gyara. Wadannan kuwa sun hada da inganta tsaro, tattalin arzikin kasa, tallafar matasa da kuma samar da ingantaccen ilimi domin gina al’umma. Sauran sun hada da bunkasa harkokin noma, farfado da masa’na’antu, samar da ayyukan yi da sauransu.
A nasa bangaren, a watan jiya ne Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam’iyyar APC. A yayin da kuma a Litinin da ta gabata ya yanki fom din takarar zaben fidda gwani na jam’iyyar, sannan kuma ya bayyana kudurorinsa da manufofin da zai aiwatar idan ya samu nasarar darewa shugabancin kasa.
A yayin da yake bayyana wa ’yan jarida kudurorin nasa a Abuja, Atiku ya ce ya yi haka ne domin kullum a shirye yake domin fuskantar kalubalen mulki, domin kada sai ya hau ya ce zai fara koyo, kamar yadda wasu ke yi.
Da yake bayyana kudurorin nasa da ya kira da taken ‘kudurori 7’ ya ce zai maida hankali wajen samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki, samar da wutar lantarki, inganta ilimi, tsaro, noma da sauransu.
A wata tambaya da aka yi masa, ta yaya za a yi ya samu nasarar dabbaka wadannan kudurori a kasar nan, shi ne ya amsa da cewa: “Na tuno lokacin da muke kan mulki, na shaida wa shugabana, Shugaban kasa cewa, yallabai akwai kungiyoyin Mafiya guda biyu a kasar nan. Ta daya, NEPA (PHCN), ta biyu NNPC. Har sai ka karya wadannan kungiyoyin Mafiya sannan al’amura za su tafi yadda ake bukata, in ba haka ba babu wani abu da zai iya aiki. Sai dai abin takaici, har zuwa yanzu, mun kasa karya wadannan kungiyoyin Mafiya da suka kanannade kamfanin samar da lantarki na PHCN, wanda har zuwa yanzu ya hana mu samun wadatattar wutar lantarki, haka shi ma kamfanin NNPC.”
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso, shi ne dan takara na uku da ake sa ran zai fafata da sauran biyun, a zaben fitar da gwani da ake sa ran gudanarwa a watan Disamba mai zuwa a jam’iyyar APC.
Binciken Aminiya ya tabbatar da cewa, wasu jiga-jigan APC sun yi kokarin sasanci tsakanin Janar Buhari da Kwankwaso, ganin cewa daga yanki daya suka fito (Arewa ta yamma), amma ba a samu haka ba. Dalili ke nan shi ma Gwamna Kwankwaso ya kaddamar da nasa taron nuna bukatar takarar a jiya Alhamis, a Abuja.
A yayin da yake magana game da takarar Kwankwaso, daya daga cikin jami’an yakin neman zabensa, Cif Olisaemeka Akamukali, ya shaida wa majiyarmu cewa: “Gwamna Kwankwaso ya kammala rangadin tuntuba da ya gudanar a duk fadin kasar nan, don haka yanzu ya shirya fafata takarar neman shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar APC. Shigowarsa takarar, babu shakka zai canza alkalumman siyasa a kasar nan.”
Da yake karin bayani game da yadda bukatar Buhari za ta shafi Kwankwaso, Cif Olisaemeka ya ce ya dace Janar din ya taimaka wa sabbin jini su jaraba sa’arsu: “Hakika mun yarda cewa Buhari mutum ne adali amma kuma ya kamata a fahimta da cewa shekaru sun fara yi masa yawa. Yanzu shekarunsa 73, yana kan zuwa 74. Shi kuwa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya kusa kai wa 70 amma Kwankwaso zai cika shekara 58 nan da 21 ga Oktoban bana, don haka shi ke da kuruciya a jikinsa; shi ya fi dacewa da takarar nan.” Inji shi.
Haka kuma ya kara da cewa ba gaskiya ba ne da wasu ke cewa wai Kwankwaso ba zai iya fafatawa da tsoffin ’yan siyasa ba. Ya ce gwamnan yana da kwarewa a siyasance domin tun daga 1991 ya fara haskakawa a siyasa, lokacin da ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Ta Tarayya a karkashin tsohuwar jam’iyyar SDP.
“Kwankwaso ya taba zama dan majalisa, ga shi gwamna har sau biyu kuma tsohon minista. A lokacin da ya yi takarar gwamna a Jihar Kano bai ci ba, ya taya wanda ya kayar da shi murna, ya jira tsawon shekara takwas, sannan ya sake dawowa ya kada jam’iyyar da ke kan mulki.”
Baya ga wadannan zaratan ’yan takara uku da ke zawarcin APC ta amince wa daya ya yi takarar shugabancin kasa, akwai wasu ma da suka tagaza. Akwai tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki, wanda a Lahadin da ta gabata ce ya sanar da janyewarsa daga takarar. A yayin da wasu ke zargin cewa ya janye ne don Buhari. Shi kuwa Janar ya karyata wannan batu a Ilorin, ya ce bai roki Bukola alfarmar ya janye masa ba.
Janar Buhari ya jaddada cewa duk da cewa ya amince da duk matakin da jam’iyyarsu za ta dauka game da takarar, ko dai a yi sulhu tsakaninsu ko kuma a yi zaben fitar da gwani. Sai dai ya ce ya fi son a bar al’umma su zabi mutumin da zai shugabance su da kansu.
“Na karanta a jarida cewa na roke shi ya janye mini. Ban roki Saraki ya janye mini ba, abin da ya yi, zabi ne na kashin kansa. Ya taba zama gwamna, yana da ilimin siyasar kasar nan. Mahaifinsa ya yi aiki tukuru wajen gina daular siyasa, wacce al’ummar jiharsa ke ba goyon baya.”
Wani dan takarar kuma da ake ganin zai shiga zaben fitar da gwanin, shi ne Mista Sam Nda Isaiah, wanda ake sa ran nan gaba kadan shi ma zai kaddamar da nasa taron nuna bukatar.
A yayin da ake sauraren ranar gumurzu da fafata zaben fitar da gwani a Disamba mai zuwa, tsakanin ’yan takarar, wasu na ganin cewa akwai yiwuwar zaben ya haifar da matsala a jam’iyyar. Kodayake kwanakin baya a Kaduna, an ji Janar Buhari yana rokon magoya bayansa da su ba duk wanda ya samu tikitin tara goyon baya daga cikinsu. Ko haka za ta tabbata? Lokaci ne zai tabbatar.