✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talaka ba ka da maigadi

Allah Sarki talakan Najeriya, ba mu da maigadi, bare shugaba. Babu ruwa, babu wuta ga talauci ya ishe mu. Sai ga wasu daga cikin masu…

Allah Sarki talakan Najeriya, ba mu da maigadi, bare shugaba. Babu ruwa, babu wuta ga talauci ya ishe mu. Sai ga wasu daga cikin masu halin da aka tura taron kasa suna neman janyewa, saboda asusunsu bai yi lodi ba. To Allah Ka gyara mana kasa da shugabanninmu. Daga Hajiya Lami 08027087462.

Gargadi ga iyaye
Assalamu alaikum. Babban Edita, don Allah ku mika mini gargadina ga iyayen ‘yan mata, kan su rika aurar da su a lokacin da ya dace Domin ‘yan mata na girma da yawa. Daga Hafsa Usman Bauchi, Aminiyar Aminiya 08109967691.

Ga dangote
Don Allah muna neman dangote ya taimake mu ya yi bayani, kan ko taliyar Spaghetti dangote da fulawar rogo ko ta alkama ake yinta? A taimaka a yi sanarwa a rediyo, saboda ba kowa ke iya sayen Aminiya ba. Na yi wannan ne saboda mu masu ciwon siga. Da fatan za a taimaka. Daga Hajiya Hindatu Kt. 08178484832.

A kawo Aminiya Bichi
Salam. Ina son Aminiya ta zama Aminiyata. Shawarata ga Aminiya don Allah dilllanku su rika sayar da Aminiya a bakin kasuwar Bichi, don samun saukin ga masu saya, ba sai an je Kano ba. Da fatan za a duba. Daga Sayyada Fatima Bichi 08181862470.

Ga masu addu’ar jarabawa
Salam Editan Aminiya, don Allah ka isar min da sakona ga wadanda suke taya mu addu’ar cin jarabawa. Kada ku gaji da taya mu addu’a. Domin yanzu (WAEC & NECO) sai da addu’a. Daga kanwar Maikawo Kano. 09030744475.

Shawara ga maza
Nakan yi mamakin maza a lokacin da budurwa t ace ba ta son su. Mafi yawancin maza ba sa tunanin cewa idan ka rasa wani abu, yakan zame maka alheri. Idan har ka yi imani da Allah. Amma za ka ga namiji yana son mace, don ba ta sonsa, shi ke nan ya manta da Allah, har ma wani ya yi mata asiri don kada ta yi aure. Ina imaninku yake? Ku rika rokon Allah Ya yi muku zabi mafi alheri a addininku da rayuwarku mana. Daga Sayyada Fatima 08133751208.

Ga Sardaunan Kano
Edita albarkacin ranar Juma’a, ina bai wa wanda na bata wa rai hakuri, ka taimaka ka isar da gaisuwata ga Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau. Daga Ummi Giginyu 09061667754.

Muna tare da Kwankwaso
Salam Edita ka mika min gaisuwata ga Gwamnan Gwamnoni, jagoran ‘yan biyar. Dokta, kuma Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso. Daga Ameena Giginyu 07039385327.

Makaranta Aminiya mata
Ga dukkan makaranta Aminiya mata, ina mika godiyata a gare ku da bangajiya, taronmu na makaranta mata Aminiya na Zariya. Daga Hajiya Fatima Zariya. 07068273657.

Ta’aziyyar mutanen Maiduguri
Assalamu alaikum. Aminiya don Allah ku mika min gaisuwar ta’aziyya ga ‘yan uwa Musulmi wadanda ke kashewa a Maiduguri. Allah Ya jikan wadanda suka riga mu Gidan gaskiya. Daga Ummi Tudun Wada Zariya 07068743172

 ‘Yan kwallon Kwankwasiyya
‘Yan kwallon Kwankwsiyya da Malam-madori SP Academy, hakika kungiyar kishin APC da ta shirya wannan wasa ta yi rawar gani. Muna fata wasannin motsa jiki su rika zama wurin hada kan matasa, ba wurin shaye-shaye da tayar da tarzoma ba. Daga Umar danHadeja 08023122946.

Shema ya gyara karatun allo
Edita don Allah ka ba ni dama in shaida wa diyan Dikko masu albarka cewar bincike ya nuna Gwamna Shenma ya fi gwamnoni taimaka wa karatun allo, daga 2007 zuwa yau, duk wata yana ba da Naira miliyan 60, don inganta karatun allo mai dimbin daraja. Dattijo Malam Mai Gambarawa ne shugaba. Mun gode Shema, shugaba nagari abin koyi gare mu. Daga Amiru Isa Bakori. 08075959086.

Gwamnatinmu ta Almajirai ce
Assalamu alaikum. Editan Aminiya. Mu gwamnatinmu Almajirai take ciyarwa, ta bar ‘yan gari da yunwa. Don tsabagen adalci, inda take fidda fiye da Naira miliyan 30 duk wata. Aaa! Lallai, mun gan su a fili sai kiba suke yi, an daina barace-barace gidajen al’umma. Daga Zakiyu Mu’awiyya Katsina 08094409707.

Ga Gwamna Shema
Editan Aminiya ka ba ni dama in yi kira ga Gwmanan Jihar Katsina, Ibrahim Shema da ya gyara mana hanyar da ta tashi, tun daga karamar Hukumar Sandamu, har zuwa garin Babban Mutum, saboda wannan hanya ta dade tana barazana ga rayukan al’umma da dukiyoyi. Da fatan Maigirma Gwamna zai taimaka mana. Daga Abubakar Lawal  Abubakar Daura 08082485297.

Ga MTN
Assalamu alaikum don Allah Edita a gaya wa MTN suna cutar da ni, saboda suna aiko mini da sakonnin tes, wanda ba na so. Na-yi na-yi su daina, sun ki. Daga Sabo No. 12 Unity Kanmo 08167943084.

Shawara ga Aminiya
Don Allah Aminiya idan kun zo jin ra’ayoyin jama’a, ku rika duba wayayyun masu ilimi da shekaru, don dama ko ba komai shekaru ma ilimi ne, ko ba boko. Nagode. Daga 07053539334.

Ga Gwamna Lamido
Kira ga Gwamna Sule Lamido, don Allah a duba ilimin ‘yan Firamare, don na sha wucewa in ga yara a gindin bishiya suna karatu. A samar musu azuzuwa da kayan zama ingantattu. Da wannan miliyan 13 da za a kashe a taron Malam Aminu Kano, gara a zuba su a harkar ilimi, tun da abin da Malam ya yi ta fafutika ga talaka ke nan, tsawon rayuwarsa. A tanadi wasu kudin a gaba, wannan dai na ilimi ne. Nagode. Daga 07053539334.

Ina son PDP da Shekarau
Salam Edita duk lokacin da na turo sako na bayyana ra’ayina a kan PDP da Malam Ibrahim Shekarau, a kan kira ni ko a yi min tes na zagi. To wnanan yana kara mini son PDP da Malam Shekarau. Daga Isyaku Captain Kofa, Masoyin Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau 08085736071.

Ga Isyaku Kofa PDP
Edita ka ba ni dama in yi martani ga Isyaku Kofa. Ba PDP ba ce mutanen arewa ba sa so ba, Lema ce ta mutane da yawa, amma mun ga tana kankancewa, shi ya sa muka bar ta, muka canza sheka. Daga Isa AbdusSalam Jos 09036924062