✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tantancewar da ba a yarda da ita ba

A bara aka kama dimbin ’yan ci-ranin da suka fito daga yankin Arewa maso Yamma, a lokacin da suke tafiya a kan babbar motar tirela,…

A bara aka kama dimbin ’yan ci-ranin da suka fito daga yankin Arewa maso Yamma, a lokacin da suke tafiya a kan babbar motar tirela, jami’an tsaro da ’yan sanda suka kai su wata cibiya suka tsare su a Abuja. Laifin da aka tuhumesu da shi, shi ne ana zargin su ’yan Boko Haram ne, wadanda ke yin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, cikin ’yan shekarun nan.
Duk da cewa sun bayyana cewa ba su da hannu a harkar, sannan irin wannan kaurar a tsakanin wadannan rukuni na mutane sanannen al’amari ne a tsakanin jami’an tsaro, an tsare wadannan mutane da ke cikin damuwa da rudu, tsawon makonni, har sai da ’yan majalisar wakilai da ke majalisar kasa suka tantance su.
Tun bayan aukuwa wancan lamari, an sha samun rahotannin kwata irin waccan  a sassa da ban-daban na kasar nan, musamman a yankin Kudu maso Gabas da Neja-Dalta, inda da zarar an ga taron ’yan Arewa, sai a fara zarginsu da zama barazana ga harkokin tsaro.
Wannan salo da jami’an tsaro suka dauka, wajen warware irin wadannan matsaloli ba abu ba ne mai kyau a tsakanin mabambantan kabilun kasar nan, da kuma hadin kan al’ummar kasa ba.
Rashin warware matsalar da ke tattare da kisan gillar da aka yi wa masu sana’o’in hannu, inda jami’an tsaron asiri na “SSS” da sojoji suka kai musu hari a wani gini da ba a kammala ba, al’amari ne da ya kamata a sake bibiyarsa. Bayan an gudanar da bincike, a karkashin kwmaitin majalisar kasa da kuma wanda Hukumar Hakkin dan Adam ta kasa ta kafa, sakamako ya nuna an tafka babban kuskure bisa la’akari da bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba, ta yiwu miyagun mutane ne suka bayar da bayanan karya. Da a ce wadanda aka azabtar sun fito ne dsga wani yanki na kasar nan da ba a yi musu haka ba.
A kwanan nan ne ake yawan cutar da masu safarar shanu da ma’aikatansu da ke fitowa daga Arewa zuwa Kudu don kasuwanci, saboda amfani da bayanan nan karya.
Harkokin ’yan Boko Haram sun haifar da rashin jituwa a tsakanin al’ummomi, musamman ’yan Najeriya da ke Arewaci da abokan zamansu na Kudanci; al’amuran sun kara rincabewa ne a sanadiyyar son ran ’yan siyasa, wadanda ke amfani da wannan damar don raba kan kabilun kasar nan, ta yadda za su kai ga cimma burinsu na siyasa.
Kwanaki kadan da suka wuce, wata jarida da ake bugawa a Jihar Legas, ta bayar da rahoto daga “majiya,” inda ta yi ikrarin cewa ’yan sanda a Jihar Ribas sun kama mutum 320, wadanda ake zargin ’yan Boko Haram ne, a tsakanin iyakar Jihohin Ribas da Imo.
Amar dai yadda aka saba yi, Kwamamishinan ’yan Sanda na Jihar Ribas, Mista Mbu Joseph Mbu, maimakon ya yi bayanan da za su warware amtsalar tsaro da ake fama da ita, sai kawai ya yi bayanan da za su kara haifar da barazanar tsaro, su kuma jefa tsoro a tsakanin al’umma.
“Wannan babban al’amari ne da ya shafi tsaro,” a cewarsa, kamar yadda aka ruwaito, sannan ya ce ba zai ce komai ba, har sai an kamala bincike.
Duk da cewa Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa babu ’yan Boko Haram a kowane sashe na Ribas, sai aka kara ruruta wutar rikicin, saboda kokowar murde karfibn iko da ya dagula harkokin mulki a can.
Amma saboda rashin ingancin rahoton, wanda aka samu daga makwafciyar Jihar ta Imo, inda rundunar ’yan sanda ta bayar sanarwar, aka ruwaito a daya daga cikin jaridu, wadanda ba su fito a jaridar Legas ba, an tabbatar da cewa duk wani bayani da ke nuni da akwai ’yan Boko Haram a wannan yanki da aka ruwaito karya ce.
A cikin bayanan da suka fito daga rundunar ’yan sandan Jihar Imo, dauke da sa hannun mai Magana da yawun rundunar DSP Joy Elemoko, cewar akwai dimbin matasa da aka dauko su daga sassan kasar nan, aka yi musu sansani a Kwalejin Horar da kwararru ta Jihar Imo, da wasu sassan jihar, da ake ba su horo, ta ce wadannan a cikin su babu masu harbin dauki daidai.
Salon da wani bangare na jami’an tsaro ke bi don tantance ’yan Boko Haram, saboda kawai sun fito daga wani sashe na kasar nan a bayyane yake karara akwai son rai a cikinra. Dole ne a daina.