✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarayyar Turai ta horar da sarakuna kan hanyoyin magance rikice-rikice

kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Cibiyar Al’adu ta Birtaniya (British Council) da kuma Gidauniyar Sulhu ta Najeriya (MCN) sun koyar da sarakunan gargajiya kimanin 300…

kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Cibiyar Al’adu ta Birtaniya (British Council) da kuma Gidauniyar Sulhu ta Najeriya (MCN) sun koyar da sarakunan gargajiya kimanin 300 kan hanyoyin yin sulhu domin magance matsalolin rikice-rikice a yankunan Arewa maso Gabas.

Shugaban Gidauniyar MCN a Jihar Adamawa, Malam Abdulkadir Bello ne ya bayyana haka a ranar Litinin lokacin da suke gudanar da taron sarakunan gargajiya da masu unguwanni domin sanin yadda za a sulhunta a tsakanin jama’a wanda aka gudanar a otel din Duragi da ke Yola fadar Jihar Adamawa.

MalaM Abdulkadir Bello ya ce gidauniyar Green Horizon ce da kungiyar EU da Cibiyar Al’adu ta Birtaniya suka dau nauyin taron domin kara wa sarakunan gargajiya fahimta a kan yadda za su sulhunta matsalolin gado da satar kayan gona da kuma fadace-fadace.

Shugaban Gidauniyar MCN ta kasa, Dokta Ukoha Ukiwo ya ce ya kamata a koyar da sarakunan gargajiya da limamai da fastoci da sauransu kan hanyoyi mafiya sauki na gudanar da sulhu domin magance matsalolin da suka shafa Arewa maso Gabas.

Galadiman Adamawa, Alhaji Lawal Ahmadu Ribadu wadda ya wakilci Lamidon Adamawa, Alhaji Barkindo Aliyu Mustapha ya ce ya yi farin ciki game da wannan taron da aka hada domin taron zai kara haske ga hakimai da dagatai da masu unguwanni sanin hanyoyi da suka dace don magance matsaloli da dama.

Farfesa Aminu Gurin na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce gidauniyar ta yi nasarar yin sulhu sau 457 a tsakanin watan Janairu da Maris din bana.

Ya kirayi sarakuna da shugabannin al’umma su yi koyi da sarakunan da aka koyar domin samun ci gaba da kwanciyar hankali a kasa baki daya.