✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffin gwamnoni 10 da ka iya tsintar kansu a kurukuku

Hukunta tsohon Gwamna Orji Kalu na Jihar Abiya da kotu ta yi kan almundahanar Naira biliyan 7.6 ya kara wa Hukumar  EFCC tagomashi. Masana shari’a…

Hukunta tsohon Gwamna Orji Kalu na Jihar Abiya da kotu ta yi kan almundahanar Naira biliyan 7.6 ya kara wa Hukumar  EFCC tagomashi.

Masana shari’a sun ce shari’ar Kalu ba ta samu tsaiko ba ne  tun shekarar 2015, sakamakon dokar Gudanar da Shari’ar Manyan Laifuffukka (ACJA) da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya sanya wa hannu.

Dokar ACJA ta sanya ala tilas dukkan bangarori biyu da ke jayayya a kotu kan manyan laifuffuka cewa ba su da hurumin kawo tsaiko ga gudanar da shari’ar ta hanyar yawan daukaka kara ko gabatar da hanzari gaban kotun da zai sanya a jingine shari’ar.

Bayan rattaba hannu a kan sabuwar dokar ta ACJA, akalla tsofaffin gwamnoni hudu ne aka zartar da hukunci a kansu. Sun hadar da Bala Ngilari na Jihar Adamawa, sai dai daga bisani Kotun Daukaka Kara ta wanke shi. Sai kuma Jolly Nyame na Jihar Taraba da Joshua Dariye na Jihar Filato sai kuma Kalu na Jihar Abiya.

Ga dukkan alamu akwai tsofaffin gwamnoni da mai yiyuwa kaddarar zaman jarun ta fada kansu tsofaffin gwamnonin sun hada da:

Sule Lamido

Alhaji Sule Lamido, wanda ya mulki Jihar Jigawa daga 2007 zuwa 2015, a yanzu yana fuskantar shari’a gaban wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja tare da ’ya’yansa biyu Aminu da Mustapha kan zargin sama-da-fadi da Naira biliyan 1.35.

Hukumar EFCC, ta yi zargin cewa a ranar 11 ga Disamban 2012 da 18 ga Disamban 2009 an karkatar da akalar Naira biliyan 1 da miliyan 356 da dubu 223 da 854.da kuma Naira miliyan 583 da dubu  785 da  81 daga lalitar Gwamnatin Jihar Jigawa zuwa asusun Sule Lamido. An kuma karkatar da wasu kudi da yawansu ya  kai Naira miliyan 206 da dubu 463 da 210 da Naira miliyan 6, dubu 288 da 947 a ranar 6 ga Fabrairun 2013. Da cekin wasu  kudi sama da Naira miliyan 24 da aka biya wani kamfanin mai suna, Speeds International, wanda Lamido ya sanya hannu. An dai gabatar da shaidun hakan a gaban kotun.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta dage sauraron karar zuwa 18 da 19 da  20 ga Fabrairun badi.

 

Murtala Nyako

Nyako, tsohon Gwaman Jihar Adamawa daga 2007 zuwa tsige shi a 2014. Tsohon Babban Hafsan Sojan Ruwan Najeriya ne kuma tsohon Gwamnan Soji a Jihar Neja.

Yana auren Mai shari’a Binta Nyako Shugabar Babbar Kotun Tarayya. Nyako da wadansu mutum 8, ciki har da dansa  Sanata Abdul’aziz Nyako da wasu kamfanoni biyar suna fuskantar zargi 37 da suka hada da cin amana, sata da wadaka da dukiyar jama’a.

Suna fuskantar shari’ar ce a gaban Mai shari’a Okon Abang kan zargin sama da fadi da Naira biliyan 29.

A ranar 5 ga Nuwamba ne EFCC ta gabatar da shaidarta na karshe, Mista Kobis wanda ya gabatar da shaidarsa ta bidiyo daga birnin Landan na Birtaniya.

 

Ayodele Fayose

Fayose, tsohon Gwamnan Jihar Ekiti daga 2003 zuwa tsige shi a 2006. Daga nan ne ya fada komar EFCC inda ta gurfanar da shi a wata Babbar Kotun Tarayya kan zargin karkartar da Naira  miliyan 860. A sa’ilin da ake ganiyar shari’ar, Fayose, ya sake samun nasarar zabensa a matsayin Gwamnan Jihar a 2014, wanda hakan ya sa aka sarara masa sakamakon rigar kariya daga fuskantar shari’a.

Sai dai, a ranar da ya mika mulki, 16 ga Oktoban 2018, EFCC ta sake gabatar da shi kan wata sabuwar tuhumar karbar Naira  biliyan 6.9 daga tsohon Ministan Tsaro, Musiliu Obanikoro, a kakar zaben Gwamnan Jihar na 2014.

An ce kudin sun fito ne daga asusun Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawarwari kan Tsaro na lokacin, Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya).

EFCC ta gurfanar da Fayose da kamfanoninsa gaban Mai shari’a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan tuhume-tuhume 11 da suka hada da sama-da-fadi da satar Naira biliyan 6.9.

 

Saminu Turaki

Turaki wanda tsohon Gwamnan Jihar Jigawa ne daga 1999 zuwa 2007, Hukumar EFCC ta zarge shi da damfarar Naira  biliyan 36 a tuhume-tuhume 32 gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa a 2011.

Daga baya an sake gurfanar da shi tare da wasu kamfanoni uku gaban Mai shari’a Nnamdi Dimgba na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a 2017.

 

Jonah Jang

Jang, wanda tsohon Gwamnan Jihar Filato ne kuma tsohon Sanata, yana fuskantar shari’a kan zargin satar Naira biliyan 6.3.

Yana fuskantar shari’ar ce a gaban Mai shari’a Daniel Longji na Babbar Kotun Jihar tare da tsohon kashiyan ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Mista Yusuf Pam.

EFCC tana zarginsu da laifuffuka 12 kan almubazzaranci da kudin gwamnati.

A zaman karshe da aka yi ranar 4 ga Nuwamban bana, shaidar EFCC, Musa Sunday, ya yi bayanin yadda kashiyan Gidan Gwamnatin Jihar ya mika wa Jang Naira miliyan 750 a lokacin yana Gwamna.

 

Babangida Aliyu

Aliyu tsohon Gwamnan Jihar Neja daga 2007 zuwa 2015, wanda ya zabi a rika kiransa da ‘Babban Hadimin’ Jihar Neja lokacin da yake mulki, yana fuskantar shari’a kan almubazzaranci da Naira biliyan 2.

Tsohon Gwamnan na fuskantar shari’a ce a gaban Mai shari’a Mika’ilu Abdullahi na Babbar Kotun Jihar, inda EFCC ta gurfanar da shi tare da Shugaban Ma’aikatan lokacin mulkinsa, Umar Nasko da kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar, Tanko Beji, kan kararraki bakwai da suka hada da cin amana.

Sauraron karar na karshe, an yi shi ne a ranar 7 ga Nuwamban bana..

 

Gabriel Suswam

Suswam tsohon Gwamnan Jihar Binuwai daga 2007 zuwa 2015, yana fuskantar shari’a ce tare da Kwamishinan Kudi na Jihar a lokacin mulkinsa, Omadachi Oklobi; kan tuhumar almundahanar Naira biliyan 3.1.

Suswam, wanda yanzu Sanata ne mai wakiltar Arewa maso Gabas na Jihar Binuwei  da Kwamishinan suna fuskantar tuhume-tuhume guda tara a gaban Mai shari’a  Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya a Abuja.

Suswam da tsohon kwamishinan tun farko an gurfanar da su ne gaban Mai shari’a Ahmed Mohammed, wanda a watan Yulin bana ya tsame hannunsa daga shari’ar; sai dai an sake gurfanar da su gaban Mai shari’a Abang ranar 30 ga Satumban bana.

 

Gbenga Daniel

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, yana fuskantar shari’a kan zargin almundahanar Naira miliyan 200 a gaban Mai shari’a Olarenwaju Mabekoje na Babbar Kotun Jihar Ogun da ke Abeokuta.

Daniel, wanda ya mulki jihar daga 2003 zuwa 2011, an gurfanar da shi ne a Oktoban 2011 kan zarge-zarge 16 da suke da nasaba da kuruciyar bera tare da almubazzarnci.

A ranar 17 ga Mayun bana, alkalin kotun ya bukaci Gbenga Daniel ya fara gabatar da kariyarsa a gaban kotun.

 

Adebayo Alao-Akala

Alao-Akala, tsohon Gwamnan Jihar Oyo ne da ke fuskantar shari’ar cin hanci da almundahanar Naira biliyan 11.5 a gaban Mai shari’a Olalekan Owolabi na Babbar Kotun Jihar da ke Ibadan.

Da farko an gurfanar da shi  ne a gaban Mai shari’a Moshood Abass ranar 11 ga Oktoban 2011.

Yana fuskantar shari’a tare da Kwamishinansa na Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Hosea Agboola da wani dan kasuwar Ibadan, Femi Babalola kan zarge-zarge 11 da EFCC take musu.

Ana zargin Alao-Akala da bayar da kwangilar gina hanya kan Naira biliyan 8.5 tsakanin 2007 da 2009 ba tare da saka aikin a kasafin kudi ba ga wani kamafani mai suna, Pentagon Engineering Serbices, wanda aka gano yana da alaka da Babalola.

 

Ikedi Ohakim

Ohakim, tsohon Gwamnan Jihar Imo ne daga 2007 zuwa 2011, yana fuskantar shari’a a gaban Mai shari’a Babatunde Kuadri na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

An fara gurfanar da shi ranar 8 ga Yulin 2015 a gaban mai shari’a Adeniyi Ademola. Sai dai bayan tilasta wa mai shari’a Ademola ajiye aiki da Hukumar Harkokin Shari’a ta Kasa NJC, ta yi – an sake saurarar karar daga farko a gaban Mai shari’a Kuadri.

Hukumar EFCC tana tuhumar Ohakim  da laifuffuka uku, inda take zarginsa da sayen wani fili mai lamba 60 kan Titin Kwame Nkurumah, a Unguwar Asokoro da ke birnin Abuja, kan  Dalar Amurka miliyan 2.2, wanda hakan ya ci karo da dokar haramta almundahanar kudi.