✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UNILAG: An rantsar da kwamitin binciken rikincin shugabanci

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya kaddamar da kwamitin binciken rikicin shugabancin Jami’ar Legas (UNILAG) da nufin lalubo hayoyin kawo zaman lafiya mai daurewa a jami’ar.…

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya kaddamar da kwamitin binciken rikicin shugabancin Jami’ar Legas (UNILAG) da nufin lalubo hayoyin kawo zaman lafiya mai daurewa a jami’ar.

A lokacin da yake rantsar da kwamitin a Abuja, ranar Laraba, Ministan ya ba kwamitin mako biyu ya gabatar masa da rahoto, sannan ya kalli rahoton karamin kwamitin zartarwa da ya binciki abubuwan da suka faru a jami’ar daga watan Mayun 2017, tare da ba wadanda ake zargi damar kare kansu kafin ya ba gwamnati shawarar da ta dace.

Kwamitin zai kalli matakan da hukumar Jami’ar ta bi na cire Shugabanta Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, ko suna kan ka’ida tare da ba shi damar kare kansa.

Zai kuma binciki ko hukumar jami’ar ta bi ka’ida wajen zabar sabon shugaban jami’ar, sannan ya ba da shawarwarin hanyoyin wanzar da zaman lafiya da lumana da kuma shugabanci na kwarai a jami’ar.

Ministan ya kuma roki masu ruwa da tsaki a UNILAG da su ba kwamitin cikakken goyon baya domin ya gudanar da aikinsa a tsanake.

A nashi bayanin, shugaban kwamitin, Farfesa Tukur Sahad, ya ba da tabbacin aiki tukuru domin samar da zaman lafiya a jami’ar. Ya kuma nemi goyon bayan kwamitin zartarwa da hukumar makarantar a yayin gudanar da aikin.

Sauran ‘yan kwamitin su en Adamu Usman na UBEC; da Farfesa Ikenna Onyedo; da Tsohon Shugaban Jami’ar Aikin noma ta Umudike, Farfesa Ekanem Braid; da Tsohon Shugaban Jami’ar Kuros Riba Farfesa Victor Onoha; da Alhaji Jimoh Bankole; da Misis Grace Ekenem.