✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waka a wurina sana’a ce – Mawaki Sarfilu

Ko za ka gabatar da kanka? An 3haife ni a garin Zarewa a Unguwar Sabon Fegi. Na yi makarantar firamre amma daga nan ban ci…

Ko za ka gabatar da kanka?

An 3haife ni a garin Zarewa a Unguwar Sabon Fegi. Na yi makarantar firamre amma daga nan ban ci gaba ba sai na koma karatun addini. Na tafi makarantar allo. Mahifina a garin Zarewa yake amma haifaffen garin Falgore ne da ke cikin karamar Hukumar Rogo da ke jihar Kano. An kai ni garin da kannensa ke zaune inda aka danka ni a wurin Malam Musa Maitalata a garin Falgore. Da farko ban yi karatun zamani mai zurfi ba amma daga baya na koma karatun boko a yanzu ina kwalejin nazarin fasaha da ilimin addini da ke unguwar Hausawa.Sannan burina na karanci Harshen Hausa a jami’a don na bunkasa harshena.

Ya aka yi ka tsunduma cikin harkokin waka?

Gaskiya ni ba gadar waka na yi ba amma tun ina yaro idan na ji wakar mutum sai kawai na kama yinta. Kuma ni bana jin kunya na rika yin waka. Ko lokacin da nake Falgore nakan bi abokanaina almajirai bara sai na rika yi musu waka ana ba mu kudi. Duk inda na yi waka sai a bamu kudi.Na yi shekaru kimanin tara ina waka.

Wadanne nau’in wakoki ka yi?

Babu fannin da ba na waka. Ina wakokin aure da ta soyayya da ta ta’aziyya da ta siyasa da sauransu. A yanzu ina da wakoki kimanin 95 wadanda na yi a rayuwata. Na yi wakar “Ina son ki Hadiza Gabon” da wakar “’Yar Fara” da wakar “dan Hausa” da sauran wakoki masu yawa. Amma gaskiya wakar da na lura mutane son fi so ita ce wakar “dan Hausa” da wakar “Mu kwana lafiya mu tashi lafiya” da kuma wakar “Hadiza Gabon”.

Me ya sa ka zabi Jaruma Hadiza Gabon daga cikin dinbin jaruman masana’antar finafinai ta Kannywood ka yi mata waka?

Ka san ita a rayuwa shi dan adam kowane mutun akwai abin da yake burge shi.Yanzu idan ka ji labarin wani mutum yana da mutunci ko yana taimakon al’umma sai kawai ka ji kana kaunarsa a zuciyarka. To ni dai ina mutukar kaunar Hadiza Gabon. Domin ita Hadiza tana da mutunci da kima a cikin jama’a. Saboda haka ni dai ina mutukar son Hadiza Gabon so na soyayya yadda da zan sami damar aurenta da na aureta. Na sanya wa wakar sunan “Ina dada son ki Hadiza Gabon”. Kuma a lokacin da zan yi mata wakar ba ta san zan yi wakar ba. Na yi mata wakar saboda Allah ba saboda son duniya ba. Saboda kaunar da nake yi mata tsakani da Allah. Da akwai baitin da na ce don tsananin son da nake yi miki da zan baki miliyan kasha shagalinki.

Bayan ka yi mata wakar me ya biyo baya?

A lokacin da na yi wakar sai na sami labarin ta tafi kasar Amurka. Wata rana sai wata murya ta kira ni ta ce tana so na yi mata wakar aure ta nemi mu hadu a hanyar Hadeja. Daga bisani bayan mun hadu sai ta ce ita ce Hadiza Gabon ni kuma na ce ni ne Sarfilu. Sai ta tambaye ni me nake so? Sai na ce mata ai ni ganinki ya fi mani komai. Bayan mun dauki hoto da ita da jama’a. Sai wani ana ce masa Salisu danfulani ya ce ka ga wannan babur din Hadiza Gabon ce ta saya maka. Sai na ce wa Hadiza ya za ki yi mini haka sai ta ce kai ma lokacin da ka yi mini waka ka yi ne saboda Allah shi ya sa ni ma na saka maka da wannan babur din. Sabon babur ne na zamani wanda samari suke ce masa roba-roba. Shi ke nan sai na karbi mukullin babur din na yi mata godiya. Sai ta kawo Naira dubu hamsin ta bani. 

A yanzu idan da Haidza Gabon za ta amince ta aure ka, ya za ka ji?

Gaskiya zan yi mutukar murna da farin ciki saboda Hadiza mace ce mai ladabi da biyayya da kima da sanin ya kamata tare da girmama jama’a.

Wadanne nasarori ka samu a sana’arka ta waka?

Na samu nasarori masu yawa. Ci da sha duk da waka nake samu. Kuma yadda duk wani mai sana’a yake tunkaho da sana’arsa haka ni ma nake tunkaho da sana’ar waka don ta rufa mini asiri a duniya. Akwai wani abu da za ka ji mawaka suna cewa wai su ba su dauki waka sana’a ba, ni kuwa duk wanda ya ce bai dauki waka sana’a ba na karyata shi. Saboda duk wani abu da za ka rika yi ya kawo maka kudi har ka taimaka wa wasu sunansa sana’a. Kamar wakata ta dan Hausa da na yi na samu alheri da daukaka a tsakanin jama’a har da masana. Don bana mantawa bayan mun tashi daga wani taro inda na yi wakar dan Hausa farfesoshi da daktoci sun rika rububin karbar lambata saboda jin dadin wakar da na yi.

Wadanne kalubale ka samu?

Ba za a rasa matasala ba amma har yanzu dai nasarorin ake ta samu kalubalen bai fara zuwa ba tukuna.

Wane buri kake so ka cimma a harkar waka?

Babban burina shi ne a cikin mawakan gargajiya muna da mawaka guda biyu, Marigayi danMaraya Jos da Alhaji Mammam Shata. Fatana shi ne in wuce matsayinsu a waka. Ka ga yanzu Abubakar Ladan ba za a taba mantawa da shi ba saboda wakar da ya yi ta Afirka.

Wace waka kake aiki a kanta yanzu?

Wakar da nake aiki a akanta ita ce “Ayyare Iye nanaye”. Waka ce mai kafiya mai wahala saboda masana sun ce kafiyar “ye”ta fi kowace wahala a Harshen Hausa. Waka ce tamkar wakar Sani Sabulu ta “Salo” wacce da ya yi mutane suka rika yin mamakin yadda ya yi ta. To ni ma wakar nan idan na fito da ita jama’a za su yi mamamaki sosai.