✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Warri Wolbes za ta kece-raini da AC Leopard na Kongo

Kulob din Warri Wolbes na Najeriya zai hadu da na AC Leopard a gasar cin kofin kalubale na Afirka (CAF Confederantions Cup) a jadawalin da…

Kulob din Warri Wolbes na Najeriya zai hadu da na AC Leopard a gasar cin kofin kalubale na Afirka (CAF Confederantions Cup) a jadawalin da hukumar CAF ta fitar a ranar Talatar da ta gabata.

Jadawalin gasar ya gudana ne a ranar Talatar da ta gabata a Hedkwatar Hukumar da ke Cairo, inda ya nuna yadda aka kasafta kungiyoyin kwallo takwas wadanda suka samu nasara a zagayen farko da kuma wasu kungiyoyi takwas da ba su samu nasara ba a zagayen farko amma sun dan tagaza. Hakan ne ya sa aka hada kulob din Warri Wolbes na Najeriya da kuma AC Leopard na Kongo a wasan da za su yi a matakin zagaye na biyu.
Kulob din AC Leopard ya sha kashi ne a wajen Smouha na Masar da ci 2-1, a wasannin da suka yi gida da waje a karshen makon jiya, al’amarin da ya sa aka kasafta shi a daya daga cikin kulob din da ba su samu nasara a wasannin zagayen farko ba.
Ana sa ran kulob din AC Leopard zai hadu da na Warri Wolbes ne a tsakanin ranakun 15 ko 16 ko kuma 17 ga wannan wata da muke ciki yayin da za su sake haduwa a wasa zagaye na biyu bayan makonni biyu da yin wasan farko.
Kulob din Wolbes ne ya fitar da na MK Entranchiete na Kongo Brazabille da ci 3-1 a wasannin gida da waje da suka yi a karshen makon jiya.