✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan jaridar Najeriya sun hana ni aure – Rita Dominic

Rita Dominic, ’yar fim din Najeriya, wacce har yanzu ba ta yi aure ba, ta dora laifin rashin samun tsayayyen mijin aure ga ’yan jaridar…

Rita Dominic, ’yar fim din Najeriya, wacce har yanzu ba ta yi aure ba, ta dora laifin rashin samun tsayayyen mijin aure ga ’yan jaridar Najeriya.
Kyakkyawar ’yar fim din, wacce a makonnin baya ta yi bikin cikarta shekara 36 a duniya, ta ce tun da dadewa ta shirya kuma ta natsu domin yin aure, amma ’yan jarida suna watsa wa shirin nata kasa, domin kuwa ko ta samu saurayin, ta yi zargin sakamakon labarai marasa tushe da ake watsawa game da ita, sai lamarin ya sukurkuce.
Ta ce ko a shekarun baya, ta yi soyayya ta hakika da wani amma sai ’yan jarida suka dora mata kahon zuka. Ta ce tun daga lokacin ba ta kara samun tsayayyen manemi ba, domin kuwa koda ta samu ma, ’yan jarida za su watsar mata da gayyar.
Sai dai kuma masu kula da al’amuran da ke kai-komo a harkar fina-finai a Najeriya sun shawarci ’yar fim din da ta daina zargin ’yan jarida game da wannan batu. Sun ce idan har abokan sana’arta kamar Omotola Jalade-Ekeinde da Mercy Johnson da Ini Edo za su iya samun mazajen aure, duk kuwa da irin labaran da ’yan jarida ke watsawa game da su, ba su ga dalilin da zai sa ita ma ta rasa manemin da zai aure ta ba.