✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan takara 143 ne suka fafata a gasar karatun Alkura’ani ta Karamar Hukumar Jos

Masu takara maza da mata 143 daga rassan Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah,  reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato…

Masu takara maza da mata 143 daga rassan Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah,  reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato ne suka fafata a gasar Musabakar  karataun Alkura’ni Mai girma, karo na 23 da kungiyar ta shirya a garin Jos.

Gasar wadda aka yi kwana 4 ana gudanar da ita, an fafata ne a matakai 7, kuma Imrana Dahir ne ya zama Gwarzon Shekara a bana.

Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar reshen Jihar Filato, Hafiz Aliyu Abdulwahab ya bayyana muhimmancin karatun Alkur’ani Mai girma.

Ya ce ta hanyar Alkur’ani ne aka fahimci yadda aka wajabta yadda za a yi Sallah da yadda za a fahimci Tauhidi da yadda za a yi Zakkah da yadda za a yi Azumi da sauran abubuwan da suka shafi addinin Musulunci. Ya ce Allah da kanSa Ya ce lallai wannan littafin Alkur’ani yana shiryarwa kuma yana albishir ga masu imani. Don haka ya yi kira ga al’ummar Musulmi su tsaya wajen ganin sun tallafa wajen karantar da Alkur’ani Mai girma.

Babban Bako Mai jawabi kuma dan Majalisar Dokokin Jihar Filato na Mazabar Jos ta Arewa, Ibrahim Baba Hassan ya yi kira ga al’ummar Musulmi su ba da gudunmawa wajen ganin an daukaka addinin Musulunci. Ya ce babu shakka gasar karatun Alkur’ani Mai girma tana bukatar taimakon al’ummar Musulmi baki daya.

Dan majalisar, wanda Malam Salmanu Hassan Dikko ya wakilta ya ce da karatun Alkur’ani ake neman duniya da Lahira. Ya ce don haka duk wanda ya riki Alkur’ani ba zai tabe ba.

Tun farko a jawabin Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa Ustaz Muhammad Haris Shehu ya ce ya kamata jama’ar Musulmi kowa ya tashi ya daga Alkur’ani Mai girma, musamman wajen koya wa yara karatunsa da sanin muhimmancinsa. Ya ce idan mutane suka tallafa wa yara wajen koyon karatun Alkur’ani za a samu yara da dama da za su haddace shi.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi su ba da gudunmawa wajen tallafa wa Alkur’ani Mai girma, domin shi ne zai cece su a ranar tashin Alkiyama. Ya ce duk dukiyar da Musulmi ya tara idan bai taimaki addinin Musulunci ba, ya yi aikin banza.

A wajen gasar, an rarraba kyaututtukan kekunan hawa da akwatuna talabijin da rediyo da turamen atamfofi da yadukan shaddoji ga wadanda suka zamo zakaru a matakai  7 da aka fafata.