A yankin Banda Aceh, inda ake gudanar da shari’ar Musulunci a kasar Indonesiya, an kwace kayan wasan tartsatsin wuta da mabusa a hannun mutane, bayan hukumomin yankin sun hana bikin sabuwar shekara, a karo na farko, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito..
Tun a daren Litinin din makon nan aka fara kai farmaki a tituna da kantunan da ke sayar da kayayyakin, bayan da aka bayar da fatwa, sannan majalisar malamai ta tabbatar da haramcin sabuwar shekarar Miladiyya a birnin Banda Aceh.
Gwamnatin Banda Aceh ta ce ta dogara da wannan fatwa, shi yasa ta haramta bikin sabuwar shekarar a cikin birnin.
Yankin Banda Aceh da ake shari’a a Indonesiya ya hana bikin sabuwar shekara
A yankin Banda Aceh, inda ake gudanar da shari’ar Musulunci a kasar Indonesiya, an kwace kayan wasan tartsatsin wuta da mabusa a hannun mutane, bayan…