✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zakaru uku na gasar Alkur’ani za su wakilci Najeriya a kasashen waje

Zakaru uku da suka yi nasara a gasar Musabakar Alkur’ani da kungiyar Yada Addinin Musulunci ta Najeriya ta shirya a Abuja ne za su wakilci…

Zakaru uku da suka yi nasara a gasar Musabakar Alkur’ani da kungiyar Yada Addinin Musulunci ta Najeriya ta shirya a Abuja ne za su wakilci Najeriya a gasar karatun Alkur’ani  ta bana da za a gudanar a kasashe daban-daban na duniya.
Hafzi Ja’afar Yakubu wanda ya wakilci Abuja a gasar kuma ya lashe gasar Izifi 60 da Tajwidi a bangaren maza, shi ne zai wakilci Najeriya a kasar Turkiya, sai Malama Badiya Sulaiman ita ma daga Abuja da ta lashe gasar Izifi 60 da Tajwidi a bangaren mata, za ta wakilci Birnin Tarayya a gasar karatun Alku’ani da za a gudanar a Jihar Sakkwato.
Sai Abdullatif Yusuf daga Jihar Filato wanda ya zo na biyu a haddar Izifi 60 da Tajwidi, zai wakilci Najeriya a gasar da za a yi a kasar Masar, sai kuma Abdurrahman daga Jihar Benuwai wanda ya zo na uku a hadar izifi 60 da Tajwidi, shi kuma zai wakilci Najeriya a kasar Tanzaniya.
A bangaren Tangimi kuwa Habib Yunus daga Filato shi ne ya zama zakara, sai Mulat Muhammad daga Abuja ya zo na biyu sai Muhammad B. Adamu daga kungiyar NASFAT ta Abuja da ya zo na uku.
Shugaban kungiyar ta kasa, Dokta Muhammad Kabir Adam ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wurin rufe gasar da aka gudanar a Abuja a ranar Asabar da ta gabata.
Dokta Kabir ya ce bajintar da matasan suka nuna ita ta kai su ga samun wakilcin kasar nan a kasashe daban-daban. Ya ce kungiyar ta shirya gasar ce da hadin gwiwar wata cibiyan ta kasar Turkiya mai suna Turkiye Diyanet Foudation wacce take da alaka da ofishin Jakadancin kasar Turkiya domin bunkasa karatun Alkur’ani.
Ya ce makasudin shirya gasar shi ne don a zaburar da matasa da dalibai wajen karatun Alkur’ani.
Da yake jawabi, jami’i a ofishin Jakadancin Turkiya, Ali Kasikirik ya ce kasar Turkiya tana tallafawa sosai wajen bunkasa ilimin addinin Musulunci a Najeriya. Ya ce gasar za ta cusa wa matasa da dalibai son karatun Alkur’ani tare da yin rigegeniyar haddace shi da kuma yin aiki da shi.
Zakaran gasar Ja’afar Yakubu ya ce ya shirya tsaf don ya fafata da ’yan’uwansa mahaddata a kasar Turkiya. Ya yi fatan yin kokarinsa don zama zakara a gasar tare da fito da sunan Najeriya a duniya baki daya.
An raba kyaututtukan kudi da kur’anai ga wadanda suka shiga gasar.