✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddamar Kwankwaso da Ganduje kan sayar da kadarorin gwamnati

Tsagin Kwankwasiyya a Kano zasu shiga zanga-zangar adawa da sayar kadarori da gwamnatin Kano ke yi.

Tsagin Kwankwasiyya na jam’iyyar PDP a Jihar Kano, ta ce za ta yi zanga-zangar adawa da matakin Gwamna Ganduje na sayar da kadarorin gwamnati da wasu wuraren tarihi a jihar.

’Yan Kwankwasiyya, karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun ce yadda gwamnatin jihar mai ci ke sayar da kadarori domin biyan bukatar kanta ba daidai ba ne.

“Ta dauke Gidan Zoo daga cikin gari zuwa wani yanki wanda hakan bai dace ba, kamata ya yi a yi amfani da shawarar Kwankwaso wajen kirkirar wasu sabbi a manyan yankuna da ake da su.

“Ina ba mutanen Kano tabbacin cewa, duk wani waje da aka gina ko aka sayar ba bisa kai’da ba, wata rana sai an kwace tare da rushe ire-iren wuraren.

“Ba abin da Gwamnatin Ganduje ke yi face ruguza tarihi, don haka ba za mu zuba ido ba, za mu dauki matakin shari’a da ya dace, za mu yi zanga-zanga domin dakatar da wannan”, inji su.

Kakakin Kwankwasiyya kuma dan takarar Mataimakin Gwamnan Kano a jam’iyyar PDP a zaben 2019, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya lissafo, wuraren da ya ce bai kamata gwamnatin ta sayar ba.

Wuraren su ne; Daula Otal, Gidan Jaridar Triumph, Masallacin Idi na Kofar Mata, Sabuwar Kasuwar Yanka Dabobbi ta Panshekara, wani yanki na Masallacin Juma’a na Fagge, wani bangare na sansanin alhazai, da tashar motoci ta Shahuci.

Martanin Ganduje

A nasa bangaren, Gwamna Abdullahi Ganduje, ya ce babu wani wuri da aka sauya ko sayar, sai da aka cimma matsaya da masu ruwa da tsakin jihar, kuma hakan shi ne mafi dacewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta hannun hadiminsa kan kafafen sadarwa Salihu Tanko Yakasai.

“Komai da aka yi an yi sa ne bisa tsarin doka da shari’a kuma babu wani abu da ya saba wa doka, domin sai da aka tattauna da masu ruwa da tsaki sannan aka zartar da hukunci”, cewar Yakasai.

Ya kara da cewa in har ’yan Kwankwasiyya za su yi zanga-zanga, to dole su samu sahalewar rundunar ’yan sandan jihar, saboda gwamanti ba za yarda a fake da sunan zanga-zanga a tada hankali a jihar ba, duba da irin yadda zanga-zangar #EndSARS ta rikide.

Da aka tambaye shi game da zaluncin ’yan sanda a jihar, Yakasai ya ce Gwamna Ganduje ya ba wa Antoni Janar na jihar yin bincike tare da gabatar masa da rahoton binciken.