✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta kai hari filin jirgin saman Kandahar a Afghanistan

Taliban ta kai hari filin saboda ta nan ne gwamnati ke kaddamar musu da hare-hare.

Mayakan kungiyar Taliban a kasar Afghanistan sun harba wasu Rokoki guda uku a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kandahar a kasar.

Harin, wanda aka kai shi da sanyin safiyar ranar Lahadi a cewar kakakin kungiyar, Zabiullah Mujahid, wani yunkuri ne gurgunta yawan hare-haren da dakarun gwamnatin Afghanistan ke kai musu ta jiragen sama.

“Mun kai hari filin jirgin saman Kandahar ne saboda makiyanmu na amfani da shi a matsayin cibiyar kaddamar da hare-harensu a kanmu,” kamar yadda kakakin na Taliban ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

Rahotanni sun ce harin dai ya yi sanadiyyar soke sauka da tashin jirage da dama a filin.

Jami’an gwamnatin kasar dai sun ce harin rokokin ya tilasta musu dakatar da dukkan hada-hada a filin, kuma ya lalata wani sashe na titin da jirage kan yi gudu kafin tashi da saukarsu.

Sai dai hukumomin sun ce babu cikakkun bayanai kan ko an sami asarar rayuka sakamakon hatsarin.

Ko a ranar Babbar Sallar da ta gabata dai sai da Taliban ta kai wani hari kusa da Fadar Shugaban kasar ta Afghanistan da ke birnin Kabul.