✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin COVID-19: Majalisa ta kalubalanci Minista kan yadda ta kashe N32.4bn

Ministar dai ta bayyana ne gaban kwamitin domin yi masa bayani kan yadda ta kashe kudaden wadanda aka warewa ma’aikatarta.

Mambobin Kwamitin Ayyuka na Musamman na Majalisar Dattijai ranar Alhamis sun kalubalanci Ministar Jinkai, Sadiya Umar-Farouk kan yadda ma’aikatarta ta kashe Naira biliyan 32.4 a matsayin tallafin COVID-19.

Ministar dai tun da farko ta bayyana ne gaban kwamitin domin yi masa bayani kan yadda ta kashe kudaden wadanda aka warewa ma’aikatarta domin raba tallafin cutar a bara.

Daya daga cikin mambobin kwamitin, Sanata Ali Ndume ya ce, “Salon da ma’aikatarki ta dauka ba zai taimaka ta kowacce irin hanya ba wajen magance yanayin da kasa take ciki. Kamata ya yi in za a bayar da tallafi ya zama mutane da dama sun amfana.”

Kazalika, mataimakin shugaban kawamitin, Sanata Biobarakuma Eremionyo cewa ya yi, “Babu ta yadda za a yi raba N10,000 ko N20,00 na tsawon watanni biyu ga mutane marasa aikin yi ya magance talaucin da yake addabarsu.”

Da take mayar da martani, Minista Sadiya ta ce Naira biliyan 2.3 ne kacal aka ba ma’aikatar tata daga cikin Naira biliyan 32.4 da aka ce an ware mata.

“An ware kudaden ne domin raba N5,000 ga mutane miliyan daya masu karamin karfi na tsawon watanni shida,” inji ta.

Ta ce kasancewar har yanzu cutar ba ta tafi ba gaba daya, ma’aikatar za ta ci gaba da bullo da hanyoyin kaiwa ga irin wadannan mutanen da nufin tallafa musu.