✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya jajanta wa mutanen Rarah kan kisan mutum 9

Ya ce bai kamata mahara kusan 200 su zo kan babura da rana tsaka su yi ta’sar amma a gaza samun wanda zai jawo hankalin…

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar jajantawa ga mutanen garin Rarah dake Karamar Hukumar Rabah a jihar ranar Juma’a domin jajanta musu kan mummunan harin da ’yan bindiga suka kai musu.

Gwamnan ya nuna damuwarsa kan harin, inda ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro domin magance matsalar tsaro.

A ranar Litinin din da ta gabata ne mahara dauke da bindigogi a kan babura kusan 200 suka afkawa garin Rabah cikin karamar hukumar Rabah a jihar Sakkwato in da suka kashe mutum tara suka tafi da shanu 500.

Maharan dai sun shiga garin ne da rana tsaka suka rika harbi kan mai uwa da wabi har suka samu nasarar aika-aikar.

Rahotanni sun ce maharan sun raunata mutane da dama a garin, ciki har da wata tsohuwa da aka sanya harsashi a bakinta aka farke fatar bakinta.

Gwamna Tambuwal ya umarci Shugaban Karamar Hukuma ya rika taron majalisar tsaro domin daukar matakan da suka dace tsakanin jami’an tsaro da g’Gwamnatin Jihar.

Ya ce bai kamata mahara kusan 200 su zo kan babura da rana tsaka su yi ta’sar amma a gaza samun wanda zai jawo hankalin jami’an tsaro ba.

Gwamnan ya ce dole mutanen gari su rika taimakawa gwamnati da jamia’an tsaro ta hanyar kai rahoto muddin ana son kawo karshen matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa.