Taraba: ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace mai gari da matansa | Aminiya

Taraba: ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace mai gari da matansa

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga
    Magaji Isa Hunkuyi, Jalingo da Abubakar Muhammad Usman

’Yan bindiga sun kashe mutum hudu, suka sace wasu hudu, ciki har da Mai Garin Maigemu da matansa biyu a kauyukan Maigemu da Kwantan Nanido da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba.

’Yan bindigar sun sace mai garin da matansa biyu ne a Kwantan Nanido a ranar Talata da dare, sannan suka je suka kashe wasu mutum hudu a kauyen Maigemu.

Rahotanni sun ce maharan, wadanda suka yi kaurin suna wajen addabar yankin Kogin Binuwai, wurin da hare-ahren da suke kaiwa a bisa babura ya tilasta masunta da manoman rani kaurace wa wajen neman abincinsu.

Shugaban yankin Mutumbiyu, Alkali Sani Muhammad (mai ritaya), ya bukaci karin jami’an tsaro a yankin don tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan al’umma.

Ya shaida wa Aminiya cewa, ’yan banga na kokarin kare kauyukansu musamman a cikin dare, amma suna bukatar dauki daga sojoji.

Sai dai Kakakin ’Yan Sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, bai amsa wayar wakilinmu ba, ballantana a samu jin ta bakinsa game da faruwar lamarin.