✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarihi da rayuwar ’yan Afirka da ke kula Kabarin Manzon Allah (SAW)

A baya, kafin a ba su hakkin kula da kabarin Manzon Allah (SAW), su din bayi ne daga yankin Arewacin Habasha, amma yanzu dai labarin…

Agha su ne mutanen da ke aikin kula da kabarin Manzon Allah (SAW) da sauran ayyuka na musamman a Masallacin Haramin Makka da na Madina.

Agha (jam’insu kuma Aghawat) kalma ce da ake kiran mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu kacokam wajen yin hidimar kula da Masallatan Haramin Makkah da Madina.

Mutanen da ake kira da Agha suna da matukar muhimmanci a tarihi da kuma gudanar da Masallatan Harami.

Kalmar ta samo asali ne daga harshen Turkanci, da ke nufin babban yaya; amma su ’yan asalin yankin Arewacin kasar Habasha ne.

A baya, kafin a ba su hakkin kula da kabarin Manzon Allah (SAW), su din bayi ne daga yankin Arewacin Habasha, amma yanzu dai labarin ya sauya.

A Makkah da Madina, kalmar Agha lakabi ne na girmamawa ga wadannan hadimai na musamman a Masallatan Harami da ke biranen biyu.

Agha sukan yi shiga ce ta farar jallabiya da wando da rawani da koren damara.

Suna zama ne a wani dan daki da ke jikin inda kabarin Manzon Allah (SAW) yake a Masallacin Madina.

Ayyukan Agha

Ayyukan da Agha suke yi a baya sun kai guda 42, kamar wanke wurin da ake dawafi, kula da tsafta da kuma kunna fitilun Masallatan Harami, kula da kabarin Manzon Allah, kula Mimbarinsa a Masallacin Madina da dai sauransu.

Sai dai a yanzu aikinsu ya takaita ga karbar bakuncin Sarkin Saudiyya da kuma bakin alfarma da suka kai ziyara a Makkah da Madina.

Su suke ma shayar da manyan bakin ruwan Zamzam sannan idan bukata ta taso, su suke budewa su kuma jagoranci bakin su zuwa dakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake domin kai masa ziyara.

Bugu da kari, Aghawat ne suke aikin rabe tsakanin maza da mata a lokacin ibada a wurin dawafi.

Tarihin masu kula da Masallatan Harami

An fara sanya su wannan aiki ne tun a karni na 12, a matsayin masu rike makullai da kuma kula da dakin da karabin Manzon Allah (SAW) ya ke, da kuma mimbarinsa da dai sauransu.

Sahabin Manzon Allah (SAW), Mu’awiya dan Abu Sufyan shi ne Khalifa na farko da ya fara nada hadiman Masallacin Harami daga cikin baya.

Daga bisani dansa, Yazid ya nada wadanda za su rika kula da wasu wurare na musamman a masallacin.

Mawallafi Rafaat Basha, ya bayyana cewa Abu Jaafar Al-Mansour shi ne Khalifan da ya fara tsarin sanya Agha a matsayin hadimai na musamman a Masallacin Haramin Makkah.

A Masallacin Madina kuma sun fara aiki ne a zamanin Salahuddin Al-Ayyubi.