✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarin Fuka ya kashe mutum 149 a Kuros Riba

Mutum ɗaya mai fama da cutar ta tarin Fuka na iya baza ta ga mutum 15 a lokaci guda.

Mutum 149 daga cikin mutum 7,000 da suka kamu da cutar tarin fuka suka rasu a cikin shekara biyu da suka gabata a Jihar Kuros Riba.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Dokta HenryAyu ne ya sanar da haka a yayin ƙaddamar da gangamin wayar da kan jama’a kan cutar da kuma hanyoyin da ake ɗaukarsta domin kauce wa faɗa wa haɗarin kamuwa da ita.

Kwamishinan ya ce yanzu haka akwai kimanin mutum 177 da suke karɓar maganin cutar asibiti a sassan jihar.

A yayin da yake karin bayani dangane da cutar da kuma yaduwarta, Dokta Bassey Offor, wani ƙwararren likita a jihar ya yi bayani ne kan yadda cutar ke iya yaduwa idan ba a ɗauki kwakkwaran matakin dakile ta ba.

Kuma ya ce masu ɗauke da ita idan suka ki zuwa asibiti mutum ɗaya mai cutar ka iya baza ta ga mutum 15 a lokaci guda.

Ya ce a cikin shekara guda matuƙar ba hattara aka yi ba, kuma aka magance halin ko-in- kula kan ɗaukar matakin magance cutar musamman a karkara inda masu ita suka fi yawa, to yawan masu cutar zai karu da kuma mace-macen da ka iya faruwa.