✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashin farashin fetur daga shekarar 2016 a Najeriya

Yadda aka samu karuwar farashin man fetur daga shekarar 2016 zuwa 2020. Farashin da ya fara daga Naira 86.50 zuwa Naira 151.56.

Tun a  shekarar  2016,  farashin man fetur yake ta hauhawa inda hakan yake ta sanya ’yan Najeriya cikin wani mawuyacin hali, saboda yadda farashin yake karuwa ba tare da sauka ba.

A watan Mayun shekarar 2016, farashin man fetur ya karu zuwa Naira 145 kan kowace lita daga Naira 86.50 da kasar ta gada daga mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

A watan Maris na 2020, farashin litar man fetur ya sauka zuwa Naira 125 daga Naira 145.

A watan Mayu na 2020, Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur (PPPRA) ta sanar da karin farashin daga Naira 121.50 zuwa Naira 123.50 kan kowace lita.

Amma a watan Yuli 2020, sai farashin ya karu daga Naira 140.80 zuwa Naira 143.80.

A watan Agusta 2020, an sake samun sauyin farashin tsakanin Naira 145.86  da Naira 148.86.

A yanzu haka sauyin farashin da aka samu shi ne wanda ya karu a ranar Laraba 2 ga Satumba 2020, inda aka samu karin farashin zuwa Naira 151.56.

Yayin da ’yan kasuwa kuma suka ce za su kara nasu farashin sama da Naira 151.56.