✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tawagar shugaban kasa ta musamman ta sauka a Kano

Wata tawaga ta musamman da Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa a Kan Yaki da COVID-19 ya tura ta isa Kano don binciko dalilin mace-macen da…

Wata tawaga ta musamman da Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa a Kan Yaki da COVID-19 ya tura ta isa Kano don binciko dalilin mace-macen da aka samu a ’yan kwanakin nan, ta kuma tantance yunkurin jihar na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Tawagar ta isa jihar ne kwana guda bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi kakkausar suka a kan gwamnatin tarayya, wadda ya ce ta juya wa Kanawa baya.

Da yake magana jim kadan bayan saukar su a Gidan Gwamnatin Kano, jagoran tawagar, Dokta Nasir Sani Gwarzo, ya ce gwamnatin tarayya ba ta juya baya ga Kanawa ba.

“Dalilin wannan ziyara tamu a Kano ita ce mu yi abin da shugaban kasa ya umarce mu, ba ragi ba kari.

“Duk wanda ke kallon Najeriya a matsayin kasa ya san cewa Kano na da matukar muhimmanci saboda dalilai da dama: matsayinta ta fuskar tattalin arzkin kasa, da yawan al’umma, da ma kuma cewa ko a fadin duniya idan abu ya faru a Kano, to akwai yiwuwar ya faru a sauran sassan duniya”, inji Dokta Gwarzo.

Dokta Gwarzo, wanda kwararre ne a kan cututtuka masu yaduwa, ya kara da cewa, “A duk lokacin da wani abu ya faru a Kano, to zai ja hankali, mai kyau ne ko mara kyau, ciki kuwa har da sakwanni masu cin karo da juna.

“Amma dai umarnin shugaban kasa mai sauki ne matuka, Ya umarce mu ta bakin ministan lafiya mu zo Kano mu yi aiki da jami’an da ke kasa don gano me ake bukata ta fuskar tallafi”.

Shi ma da yake nasa tsokacin, mai ba da shawara na musamman ga ministan lafiya, Farfesa Abdulsalam Nasidi, cewa ya yi ba su je Kano don su yi gasa da kowa ba.

“Ba mu zo don mu maye gurbin kowa ba, mun zo ne don mu karfafa juna…

“Don haka abin da ke gabanmu shi ne ba tare da bata lokaci ba mu yi dukkan mai yiwuwa daga bangaren jiha da bangaren tarayya da bangaren abokan huldarmu don taka wa wannan annoba birki ta daina yaduwa a tsakanin al’ummarmu—manufarmu ta farko ke nan”, inji Farfesa Nasidi.

Shi kuwa Gwamna Abdullahi Umar ganduje cewa ya yi duk matakin da za a dauka idan babu cibiyoyin gwaji ba zai yi amfani ba.

“Kashin bayan yaki da wannan cuta, baya ga wuraren da suka dace a kakkafa, shi ne dakin bincike.

“Cibiyar gwaji ce zuciya kuma da zarar an ce zuciya ta baci to dukkan bangarorin jiki ma sun baci.

“Idan aka ce babu cibiyar gwaji, kamar yadda yanzu kusan mako guda ke nan babu, to za ka ga cewa ci gaba da gudanar da sauran abubuwan ma ba shi da amfani tun da ba za ka iya matsawa gaba ba”.

Gwamnan ya kuma ce ba zai yiwu a ce za a dauki samfur daga Kano a kai Abuja ba, saboda tafiya ce ta sa’o’i bakwai—tun da ana gyaran hanya—domin samfurin zai iya lalacewa kafin a je, saboda haka sai an dawo an sake komai daga farko.

Jihar Kano dai na da al’ummar da yawanta ya kai miliyan 20, amma tun bayan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta kafa cibiyar gwajin cutar coronavirus kusan wata guda da ya wuce ba a yi wa mutanen da suka kai 500 ba.

Karuwar mace-macen da aka gani a kwanakin nan ta tayar da hankali, inda mutane da dama suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi wani abu.

A jawabin da ya yi ranar Litinin da maraice dai, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin amfani da duk wata hanya da ta dace don tallafa wa jihar.