✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya bukaci sojoji su kawo karshen ‘yan bindiga a Arewa

Ministan ya ce Tinubu ya ba da umarnin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga.

Gwamnatin Tarayya ta umarci Babban Hafsan Soji da ya tura karin dakaru zuwa Zamfara Katsina, Kaduna da Sakkwato domin dakile hare-haren ’yan bindiga.

Wannan na zuwa ne bayan mazauna garin Gonin Gora da ke Maramar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, don nuna fushinsu kan hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

Hare-haren ‘yan bindiga a jihohin na kara kamari, lamarin da ya kai wa sojoji hari inda wasu suka rasa rayuka.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce, gwamnati umarci shugaban rundunar sojin Najeriya da ya dauki matakin dakile ta’addancin ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Matawalle, ya ce an bayar da umarnin ne domin sojoji su hada kai da sauran jami’an tsaro tare da kawo karshen rashin tsaro a jihohin.

“Kare rayuka da tabbatar da jin dadin ’yan kasarmu ne kan gaba, kuma ya zama wajibi a dauki kwararan matakai domin dakile ta’addanci da ’yan fashi a cikin al’ummarmu.

“Ingantaccen tsaro a yankin ba kawai zai kare rayuka da dukiyoyin jama’armu ba ne, zai inganta noma da kiwo, manoma za su iya noma gonakinsu ba tare da fargabar hare-hare ba, ta yadda za a tabbatar da samar da abinci da wadatar tattalin arziki a yankin.”

Matawalle ya jaddada cewa shugab Bola Tinubu ya kuduri aniyar shawo kan matsalar rashin tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya da walwalar ’yan kasar nan baki daya.

Sai dai ya bukaci ’yan Najeriya su bai wa dukkanin masu ruwa da tsaki hadin kai, don tallafa wa jami’an tsaro a yakin da suke yi da ’yan bindiga.