✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga shugabancin Hukumar Kula da Almajirai

Tinubu ya maye gurbin Sha'abar Sharada da Birgediya-Janar Lawal Ja’afar Isa mai ritaya.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sauke Sha’aban Ibrahim Sharada daga shugabancin Hukumar Kula da Almajirai da Yara Marasa Zuwa Makaranta.

Hakan dai ne zuwa ne yayin da shugaban kasar ya amince da nadin Birgediya-Janar Lawal Ja’afar Isa mai ritaya a matsayin a sabon shugaban hukumar.

Bayyana sabon nadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a.

Haka kuma, shugbaan kasar ya kuma amince da nadin Alhaji Tijjani Hashim Abbas a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin masarautu.

Janar Ja’afar Isa jagora ne nagari ya kuma taba zama Gwamnan Jihar Kaduna a zamanin mulkin soji daga 1993 zuwa 1996, yayin da Alhaji Tijani Hashim Abbas shi ne Sarkin Sudan na Kano.

Sanarwar ta ce shugaban kasar yana fatan wadanda aka bai wa sabbin mukaman za su yi mfani da gogewar da suke da ita wajen gudanar da ayyukan da aka dora musu don ci gaban al’ummar Najeriya.

Lawan Jafaru Isa da Alhaji Tijjani Hashin Abbas dukkaninsu sun fito ne daga jihar kano.

Ana iya tuna cewa, makonni kadan kafin saukar tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin shugaban hukumar.