✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya zaftare kasafin kudin tafiye-tafiyensa

Matakin ya shafi dukkan ministoci da mataimakin shugaban ƙasa da uwargidan shugaban ƙasa.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da sanarwar zaftare kashi 60 cikin 100 na adadin makarraban da za su rika yi masa rakiyar tafiye-tafiye.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da shugaban kasar ya sanar da rage yawan jami’an da za su riƙa yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai je ciki da wajen ƙasar.

Matakin ya kuma shafi dukkan ministoci da manyan jami’an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban ƙasa da uwargidan shugaban ƙasa, wadanda su ma ya ba da umarnin rage adadin jami’an da za su riƙa yi musu rakiya.

Sanarwar wadda Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban Najeriya kan harkar yaɗa labarai ya fitar ranar Talata.

A cewar Ngelale, matakin wani yunƙuri ne na rage yawan kuɗaɗen da jami’an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye.

Sanarwar ta ce yawan jami’an da za su riƙa yi wa shugaban ƙasar rakiya zuwa ƙasashen waje, nan gaba ba za su wuce jami’ai 20 ba, yayin da ’yan rakiyarsa a tafiyar cikin gida ba za su wuce jami’ai 25 ba.

Haka zalika, Ngelale ya ce Tinubu ya ba da umarnin a daina tura ɗimbin jami’an tsaro zuwa wata jiha a duk lokacin da zai kai ziyara can, maimakon haka za a riƙa amfani da jami’an tsaron da ke jihar ne kawai don tabbatar da tsaro.