✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tottenham ta kori kocinta Cristian Stellini

Newcastle ta yi wa Tottenham dukan kawo wuka.

Tottenham ta kori kocinta na rikon kwarya, Cristian Stellini inda ta maye gurbinsa da Ryan Mason wanda zai ci gaba da jibintar lamarin horas da ’yan wasanta.

Lamarin dai na zuwa ne bayan da shugaban kungiyar, Daniel Levy ya bayyana rashin amincewa da dukan kawo wuka da ta sha a hannun Newcastle da ci 6-1 a ranar Lahadi.

Stellini, wanda aka nada shi ne a watan jiya bayan tsohon mai gidansa Antonio Conte ya bar kungiyar, kuma tuni Ryan Mason ya maye gurbinsa nan ta ke.

Mataimakin Conte na dogon lokaci ya samu nasara daya kacal daga cikin wasanni hudu da ya jagoranta, lamarin ya haifar da cikas ga damar Spurs zuwa Gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

Har yanzu Tottenham na matsayi na biyar a teburin Premier amma maki shida ne tsakaninta da ta hudu kuma da sauran akalla wasa daya.