✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Daraktan hukumar DSS, Bukar Shetima ya rasu

Tsohon daraktan ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki da dama

Tsohon Daraktan Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, Alhaji Bukar Shettima, ya rasu a Kaduna.

Ya rasu da sanyin safiyar Lahadi, bayan ya sha fama da rashin lafiya tsawon shekaru.

An yi jana’izarsa da misalin karfe 1:00 na rana a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Tsohon Daraktan ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki, ciki har da Shugaban kamfanin Barbedos Group, Alhaji Kashim Bukar Shetima da kuma Shugabar bankin Unity na Jihar Kaduna, Hajiya Hamsatu Bukar Shetima.

Tuni ’yan uwa da abokan arziki da suka shiga yin ta’aziyyarsa tare sa nema masa rahamar Ubangiji.