✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Ministan lafiya Dakta Haliru ya rasu

Tsohon Ministan Lafiya na Najeriya, Dakta Haliru Alhassan ya rasu ranar Lahadi da misalin karfe 12 na rana bayan gajeruwar rashin lafiya. Dakta Haliru Alhassan…

Tsohon Ministan Lafiya na Najeriya, Dakta Haliru Alhassan ya rasu ranar Lahadi da misalin karfe 12 na rana bayan gajeruwar rashin lafiya.

Dakta Haliru Alhassan ya rasu yana da shekara 66.

Dakta Halliru ya yi fama da ciwon suga kafin rasuwarsa. Ya rasu ya bar mata daya da yara hudu.

Marigayi Halliru abokin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ne tun suna yara.

Iyalan marigayin sun ce za a binne tsohon Ministan ne a makabartar Hubbaran Shehu da ke jihar Sakkwato.