✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Sakataren PDP na Gombe ya koma APC

Ya ce ya fice ne saboda jam'iyyar ta kasa dinke barakar cikinta

Yayin da ake shirin fara yakin neman zaben 2023, tsohon Sakataren jamiyyar adawa ta PDP a jihar Gombe, Alhaji Abubakar Usman (Buba Shanu), ya fice daga cikinta zuwa APC mai mulki. 

Buba Shanu, wanda jigo ne a PDP kuma na kusa da tsohon Gwamna Ibrahim Hassan Dankwabo, ya bayyana ficewar tasa ne a wata takarda da ya aike wa shugaban tsohuwar jam’iyyar tasa na gundumar Waziri ta Arewa a karamar hukumar Dukku a jihar ta Gombe.

A cewarsa, tsohuwar jam’iyyar tasa ta kasa dinke barakar da ke cikinta balle ta fuskanci yadda za ta samu nasarar cin zaben da ke tafe na 2023.

Bayanai sun nuna Buba Shanu da dinbin magoya bayansa daga karamar hukumar ta Dukku za su sanar da kawancensu da jam’iyyar APC mai mulki da kuma yin kokarin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zabe mai zuwa.

Sanarwar ficewar jigon na PDP na zuwa ne kasa da mako guda da murabus din wani tsohon Kwamishina a gwamnatin ta Ibrahim Hassan Dankwambo daga jam’iyyar ta PDP.