✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban NLC Ali Ciroma ya rasu

Kwamared Ali Ciroma ya kasance shugaban NLC a tsakanin 1984 zuwa 1988.

Tsohon shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC, Kwamared Ali Ciroma ya rasu.

Ya rasu ranar Talata a Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sakataren Ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen Jihar Borno kuma ɗan uwansa, Ali Ibrahim Ciroma ne ya sanar da rasuwar Ali Ciroma a madadin iyalansa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Cike da alhini nake sanar da rasuwar Kwamared Ali Ciroma, tsohon Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya.

“Marigayin ya rasu ne da yammacin yau [Talata] a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

“Marigayi Kwamared Ali Ciroma ya kasance shugaban NLC daga tsakanin 1984 zuwa 1988.

Ya kuma kasance shugaban ma’aikatan lafiya na karkara na Najeriya a shekarar 1960 kafin daga bisani ta zama Ƙungiyar ma’aikatan lafiya da kasa.