Tukunyar gas din mai shayi ta kona mutum 23 a Lere | Aminiya

Tukunyar gas din mai shayi ta kona mutum 23 a Lere

    Hussaini Isah, Jos

Alummar garin Federe da ke Karamar Hukumar Lere, a Jihar Kaduna sun shiga cikin yanayin razana sakamakon fashewar tukunyar gas din wani mai shayi a garin, da ta yi sanadin kona mutum 23.

Lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis din da ta gabata.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani kan yadda lamarin ya faru, mai shayin mai suna Sulaiman Idris, wanda shi ma bayansa da fuskarsa suka kone a gobarar, ya ce mantawa ya yi bai daure tukunyar ba bayan an dura masa gas.

Ya ce da ya dawo ya ga an daure, bayan ya kunna wuta sai yaga an sami matsala, domin basu daure ta daidai ba.

Hakan, a cewarsa ta sa ya sauko da ita kasa, domin ya kwance shi, ya sa qafa ya yi, ya yi domin ya kwance, amma abin ya gagara.

Ya ce, “Ina cikin kwancewa sai ya bugo marfin gas din, sai iskar gas din ta fara fitowa da karfi, sai na yar da shi a kasa, na fita waje.

“Da naga ta tsagaita sai na sake shigowa, don na fitar da tukunyar waje, ina sa hanu sai naji yif, kamar an kama ni, wuta ta tashi, ta kama kayan jikina baki daya.

“Sai na fito da gudu zuwa gida, ina kiran jama’a a cire min kayana, aka samu aka cire min,” inji mai shayin.

Ya ce yana amfani da gas din ne wajen soya kwai da Indomie.

“Gaskiya na yi matukar bakin ciki da faruwar wannan abu, domin ban so ace wannan abu ya fara a shagona ba, amma haka Allah ya so, don haka babu yadda zan yi”.

‘Na je shan shayi abin ya ritsa da ni’

Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, wani da ya je shan shayi kuma abin ya ritsa da shi, kuma yake kwance a babban asibitin garin Saminaka, Malam Lawal Ali ya ce shi bayan ya sha shayi, a wannan shago ya fita, bakin hanya sai ya hadu da wani dan uwansa inda suka tsaya suna magana.

“Sai na ga mai shayin ya fadi ta baya, ya yi dungure, sai muka ga hayaki ya tashi sama.

“Mun juya zamu je wajensa ke nan, sai muka ga wani hayaki yazo ya bugemu sai muka ruga da gudu muna salati. Ina qoqarin cire riga, sai wani yazo ya taimaka mani, na cire rigar aka kai ni asibiti.”

Mutum 23 ne suka kone – Dagaci

A cewar Dagacin garin na Federe, Umar Babangida Ubale, ya ce wajen da rumfar mai hsayin take tasha ce, kuma yara suna sayar da abinci a wajen.

Ya ce, “A lokacin maimakon su gudu, sai suka je suna kallon me ya faru, sai silindar ta yi bindiga, iskar gas din ta watsu, ta kona mutanen da suke wajen.

“Har wadanda suke wucewa ta hanya abin ya kona su. Wasu suna wani shago suna sayayya wutar gas din taje ta same su.

“Mutum 23 ne suka kone. Waxansu sun ji mummunan rauni, fuskoki da hannaye da kafafu da kayan jikinsu duk sun kone.

“Wasu mun kai su asibitin Saminaka, wasu kuma mutum bakwai da kunarsu ta yi muni, mun kai su asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano, wasu kuma suna jinya a gida,” inji Dagacin.

Dagacin ya ce sun sami tallafi daga dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Lere, Ahmed Manur, ta hanyar daukar nauyin biyan kudaden jinyar dukkan wadanda wannan lamarin ya shafa a asibitocin da aka kai su da kuma wadanda suke jinya a gida.

Ya yi kira ga jama’a da su rika neman sanin yadda ake amfani da tukunyar ta gas don kaucewa faruwar irin wannan a nan gaba.