✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WAEC ta saki sakamakon jarrabawar bana

WAEC ta rike sakamakon dalibai fiye da dubu 200.

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire a Yammacin Afirka (WAEC), ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar bana.

Babban jami’in hukumar a Najeriya, Mista  Patrick Areghan ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Litinin a Legas.

A cewar Mista Areghan, daga cikin dalibai 1,613,733 da suka zana jarrabawar a bana, an rike sakamakon dalibai 262,803 saboda wasu dalilai da suka danganci aikata magudi.

Haka kuma, ya ce daga cikin adadin da suka zana jarrabawar, dalibai kashi 84.38 sun samu nasarar samun makin Kiredit a darussa biyar.

Sai dai ya ce kashi 79.81 na daliban ne suka samu nasarar samun makin Kiredit a darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.

Aminiya ta ruwaito cewa daliban da ke shirin kammala karatun sakandire sun shafe tsawon makonni bakwai suna zana jarrabawar daga ranar 8 ga Mayu zuwa 23 ga watan Yunin 2023.