✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wahalar Fetur: Manyan ’Yan Kasuwa Sun Sayo Lita Miliyan 300

Kungiyar Manyan Dillalan Man Fetur (MEMAN) za ta shigo da manyan jiragen ruwa guda takwas masu dauke da litar man fetur sama da miliyan 300…

Kungiyar Manyan Dillalan Man Fetur ta Najeriya (MEMAN) ta kammala shirin shigo da manyan jiragen ruwa guda takwas masu dauke da litar mai sama da miliyan 300 domin magance karancin man da ake fama da shi a halin yanzu.

Shugaban MEMAN, Huub Stokman ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai domin magance karancin man fetur ɗin da ake fama da shi a kasar.

Stokman wanda ya tausaya wa ’yan Najeriya kan bacin rai da wahalar da suke fuskanta, ya ce, “Babban abin da muka sa a gaba a matsayinmu na MEMAN shi ne dawo da kwanciyar hankali da tabbatar da samar da man fetur a ɗaukacin gidajen mai a faɗin Najeriya cikin gaggawa.

“Muna so mu tabbatar wa jama’a cewa akwai wadataccen man fetur a inda za mu ɗauko.

“Mambobinmu za su shigo da jiragen ruwa takwas masu ɗauke da lita sama da miliyan 300 na fetur a wannan makon, wanda ya zarce abin da da muka saba ɗaukowa.

“Za a tsawaita lokacin lodin man fetur a dafo-dafo da ke faɗin ƙasar nan domin tabbatar da an yi lodi ba dare ba rana gwargwadon iyawarmu.

“Abokan hulɗarmu da suka haɗa da NARTO da PTD sun ba mu tabbacin goyon bayansu wajen tabbatar da ganin fetur ya isa gidajen man da sauri kuma cikin aminci.

“Za mu tsawaita lokacin buɗe wasu wuraren da muka keɓe domom yin hidima ga abokan hulɗarmu.”

Ya ce, za a ƙara wa masu gidajen mai yawan man da ake ba su domin magance ƙarancin man cikin gaggawa.

Shugaban manyan ’yan kasuwar ya ɗora alhakin halin da ake ciki a kan abubuwa da dama, kamar rashin kyawun yanayi a teku da kuma wasu al’amurra.

“Duk da yanayin da aka tsinci kai, a ’yan kwanaki masu zuwa muna sa ran samun babban cigaba a harkar man fetur.

“Dangane da bayanan da muke samu, ba zai ɗauki makonni biyu ba. Na yi imani  za a samu mai a wannan makon,” in ji shi.