✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wahalar mai ta fara kamari a Abuja

Kasa da mako guda bayan NNPC ta ce tana da man da zai wadaci Najeriya na kwana 40

Wahalar man fetur a garin Abuja na kamari inda karancinsa ya haddasa dogayen layin ababen hawa a gidajen mai da kuma tsadar ababen hawa na haya.

Wasu masu ababen hawa da Aminiya ta zanta da su sun koka bisa tsadar man fetur din a ’yan tsirarun gidajen man da ke da ragowarsa a Birnin Tarayyar.

A wasu warere da ke birnin masu ababen hawan haya har sun fara kara farashi saboda tsadar man da suka ce na naman wuce misali.

Yawancin fasinjoji na ta kokawa gane da cewa baya ga karin kudin ababen hawan, sai sun yi da gaske suke samun abun hawan.

“Ba karin farashin da masu motocin suka yi ba ne kadai, sai da na yi doguwar tafiya a kasa kafin da kyar na samu wadda zan hau,” inji wani maaikaci.

Malam Muhammad, wanda yake shigowa aiki daga kauyukan da ke zagaye da garin Abuja ya ce, “Zan hau babur ya fito da ni bakin babban titi, sai dan mashin din ya ce min an kara kudi daga N50 zuwa N100.

“Da na tambaye shi, sai ya ce fetur na wahalar samu kuma an mayar da shi kusan N350.”

Aminiya ta iske gidan man AA Rano da ke daura da Babbar Tashar Motar Utako a rufe, amma da dogayen layi ababen hawa a kofofinta.

Wakilinmu ya lura kan famfo daya ne kacal ke ba da mai, a lokaicin kuma masu baburan haya masu kafa uku ne a ciki, suna shan mai.

Tun a ranar Jumaa alamun karancin mai suka fara bayyana a Abuja, inda wasu gidajen mai suka wayi gari a rufe, wasunsu kuma daga baya.

Hakan na faruwa ne kasa da mako guda bayan kamfanin mai na kasa (NNPC) ya karyata jita-jitar karin farashin mai tare da ba da tabbacin yana mai da zai ishi Najeriya na kimanin kwana 40.

Yankin Kudu na cikin matsin kayan abinci

Wasu na danganta karancin man na yanzu da barazanar hana shigowar motocin dakon mai daga yankin Kudanci zuwa Arewacin Najeriya.

Wasu kungiyoyin Kudanci sun yi kurarin daukar matakin ne bayan gamayyan dillalan shanu da kayan abinci ta Najeriya ta shiga yajin aikin kai kaya zuwa Kudu.

Mako guda ke nan da kungiyoyin suka fara yajin aikin a wani mataki na kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyi da ake wa alummar Arewa duk lokacin da wani rikici ya barke a yankin na Kudu.

Gamayyar kungiyoyin masu kayan abincin na bukatar Gwamnati ta biya su Naira biliyan 147 a matsayin diyyar barnar da aka yi wa ’ya’yanta a lokacin tarzomar EndSARS da rikicin kabilancin Jihar Oyo na kwanakin baya.

Rahotanni sun nuna cewa matsakin da masu kayan abincin Arewar suka dauka ya haddasa karancin nama tare da tashin gwauron zabon kayan abinci a daukacin yankin Kudancin Najeriya.