✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wankan kududdufi ya yi ajalin dan shekara 14 a Kano

An tsamo saurayin daga cikin ruwan amma tuni rai ya yi masa halinsa.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani saurayi mai shekara 14, Abdullahi Abdulrahman, wanda ya nuste yayin wanka a wani kududdufi da ke Unguwar Kabuga a jihar.

Saminu Abdullahi, Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a birnin Dabo.

  1. Irin matan da bai kamata a yi masu kishiya ba – Dr. Ahmad Gumi
  2. Yadda sababbin al’adu suke janyo tsadar aure

Abdullahi ya bayyana cewa yaron ya gamu da ajalinsa a ranar Juma’a, yayin wanka a kududdufin.

“Mun samu kiran neman agajin gaggawa da misalin karfe 5 da minti 16 na yammacin Juma’a daga wani Muhammad Kabiru, kuma nan take muka aika jami’anmu zuwa wurin da misalin karfe 05 da minti 23” in ji shi.

A cewarsa, sun samu nasarar tsamo Abdulrahaman daga cikin ruwan amma tuni rai ya yi masa halinsa.

Kazalika, ya ce sun mika gawar mamacin zuwa ga Mai Unguwar Tudun Yola, Malam Hamza Sani, kuma an yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Islama.