✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ma’aurata sun yi garkuwa da wata mata kan zargin maita

’Yan sanda sun cafke wani magidanci da ya daure wata mata da sarka na tsawon mako biyu saboda zargin ta da maita a Jihar Kwara.

Kotu ta tsare wani magidanci da ya daure wata mata a sarka na tsawon mako biyu saboda zargin ta da maita a Jihar Kwara.

Mutumin, mai shekara 40 ya aikata wannan aika-aikan ne tare da matarsa, inda suka karbi kudin fansa Naira dubu 100 daga hannun iyayen matar da suka daure.

“Binciken farko ya nuna ma’auratan da sauran masu hannu a wannnan mummunan aiki ba su san darajar rayuwar dan Adam ba,” in ji dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Zacchaeus Folorunsho.

A yayin gurfanar da magidancin a gaban kotu, dan sandan ya shaida wa alkali cewa matar tasa ta tare da sauran masu hannu a laifin.

Ya bayyana cewa wadanda ake zargin, “Sun kware wajen aikata irin hakan a yankin Karamar Hukumar Wasu ta Jihar Kwara da kewaye.”

Saboda haka ya bukaci kotu da ta tsare mutumin, ya kuma samu amincewar Alkalin kotun,  Majistare Ibrahim Dasuki.

Daga nan kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Agusta da muke ciki.