✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wuraren da aka ga watan Dhul Hijjah a Najeriya

An ga watan a Jalingo, Ilorin, Lafia, Minna da Misau da kuma Abuja a ranar Litinin 21 ga watan Yuli 2020.

Kwamitin duban wata na kasa a Najeriya, ya sanar da ganin jinjirin watan Babban Sallah na Dhul Hijjah a yammacin Litinin 21 ga watan Yuli.

Sakon da Kwamitin ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ya “samu rahotannin ganin jinjirin watan Dhul Hijjah da yammacin Litinin a sassan Najeriya.

“Wasu daga cikin wuraren su ne: Abuja, Jalingo, Ilorin, Lafia, Minna da kuma Misau.

Sakon ya kara da cewa Laraba 22 ga watan Yuli “za ta kasance ranar 1 ga watan Dhul Hijjah”, wanda shi ne watan da alhazai ke aikin Hajji a ciki, daukacin Musulmai kuma ke yin idin Babbar Sallah.

Tun da farko Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci Musulmi a kasar da su fara duban watan daga yammacin ranar ta Litinin wanda ya yi daidai da 29 ga watan Dhul Qadah, shekarar Hijiriyya 1441.

Sanarwar ta kuma bukaci wadanda suka ga watan da su sanar da sarakunan garuruwansu domin kai rahoton ga Fadar Sarkin Musulmi.

A duk shekarar Muslunci alhazai na yin hawan Arfah ne ranar tara ga watan Dhul Hijjah, sannan idin Babbar Sallah ya biyo baya a ranar 10 ga watan.

Hakan ke nuna bana a ranar Juma’a 31 ga watan Yuli ke nan Musulmi a Najeriya za su yi hawan idin Babbar Sallah, bayan alhazai sun yi hawan arfa a ranar Alhamis 30 ga watan Yuli.

A ranar tara ga wata alhazai ke taruwa a Arfa daga Mina, a kasar Saudiyya, wanda shi ne rukun mafi girma a aikin Hajji.

A wurin suke ambaton Allah tare da yin addu’o’i da sauran ibada tun daga safiya har zuwa gabanin Magariba, inda suke zuwa su kwana a Muzdalifa, kafin washegari su koma Mina domin yin jifa da yanka dabbobinsu na hadaya da aski (ga maza) da kuma ragowar ibadun aiki Hajji.

Daga ranar 10 ga watan ne bayan sauka daga sallar idi masu abin yin Layya ke fara yanka dabbobin layyyarsu har zuwa faduwar rana.

Masu damar yin Layya na da damar su ci gaba da yin haka har zuwa gabanin Magariba a ranar 13 ga watan na Dhul Hijjah.