✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Xavi ya tsawaita yarjejeniyar zama a Barcelona

Xavi ya shafe tsawon shekaru 17 a matsayin ɗan wasa a kungiyar ta Camp Nou.

Kociyan Barcelona Xavi Hernandez ya tsawaita kwantiragin zamansa a kungiyar har zuwa shekara ta 2025.

Yana kuma da zaɓin ƙarin shekara ɗaya kunshi kwantaragin, a cewar kungiyar a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Kocin mai shekaru 43 ya karɓi ragamar Barcelona kan kwantiragin shekaru uku bayan tafiyar Ronald Koeman ɗan ƙasar Holland a karshen shekarar 2021.

Tsohon ɗan wasan ƙasar Sifaniya Xavi ya jagoranci Barca a wasanni 96, inda ya samu nasara a 61, da canjaras guda 16, sannan ya yi rashin nasara a 19.

Ya lashe kambun farko a kakar wasan da ta wuce inda ya lashe kofin Spanish Super Cup sannan ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar La Liga ta 27 wanda shi ne na farko cikin shekaru huɗu.

Xavi ya shafe tsawon shekaru 17 a matsayin ɗan wasa a kungiyar ta Camp Nou da ke Catalonia, inda ya lashe kofuna 25 – ciki har da kofunan La Liga takwas da na gasar Zakarun Turai huɗu a wasanni 767.