✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kai karar shanunsa saboda rashin madara

Madarar shanun abar so ce gare ni da matata.

Wani manomi mai suna Raamaia daga kauyen Sidlipura da ke yankin Kudu maso Yammacin Indiya, ya je ofishin ’yan sanda da shanunsa hudu don gabatar da korafi.

Ya bayyana cewa, shanun sun kasa samar masa da madara kamar yadda ya rubuta a cikin takardar korafi ranar 1 ga Disamba ga jami’an a garin Holehonnur da ke kusa.

Kuma ya ce shanun suna harbin matarsa a duk lokacin da ta nemi tatsar nononsu.

Raamaia ya yi rubutu a cikin harshen Kannada da mafi yawan jama’ar yankin Karnataka ke amfani da shi wajen magana da shi a jihar da Sidlipura da Holehonnur kamar haka: “Ina kiwon shanun nan sosai.

“Madarar shanun abar so ce gare ni da matata.”

Ya kara da cewa, “Ba daidai ba ne gare ni in fara karbo madarar shanu alhali ina kiwon shanun. Don haka a yi min adalci.”

’Yan sandan sun tura Raamaia zuwa wani asibitin dabbobi da ke kusa don duba su, kamar yadda shugaban ’yan sandan yankin, Sufeta Lakshmipathi Ramachandrappa Lambani, ya sanar ta wayar tarho.

“Ma’aikatana suna ganin korafin da manomin ya gabatar abin dariya ne,” inji Lakshmipathi a cikin harshen Hindi.

Ya kara da cewa, ma’aikatan sun gaya masa cewa, suna tunanin mai yiwuwa manomin ya sha barasa ce lokacin da yake magana, saboda halin da yake ciki da kuma jin warin abu mai kama da barasa.

Bayan an rubuta korafin, jami’ai sun koma wasu ayyuka na yau da kullum. Sai dai ba da jimawa ba kafafen labarai na cikin gida suka wallafa korafin kuma labarin ya yadu kamar yadda aka yi ta bayyanawa a shafukan sada zumunta na zamani.

Wani mai amfani da shafin Twitter mai adireshin @ SelfDoubtist ya yi tambayar cewa, “Shin wani yana iya farfagandar ciyar da kare hakkin saniya gare su?”

Wani mai shafin Tiwita @ Gemini_blr, ya yi tambayar ko manomin yana kokarin samun madara ce daga bijimi?” Sai Lambani da ya ce, “Na samu wannan korafi tamkar abin dariya.