✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a yi dokar da za ta hana raba wa daliget kudi —Jonathan

Ya ce raba wa daliget kudi don su zabi mutum ba daidai ba ne

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya caccaki salon yadda ’yan takara ke ba daliget makudan kudade domin su zabe su a dukkan manyan jam’iyyun kasar.

A ’yan kwanakin nan dai rahotanni sun bayyana yadda ’yan takara ke biyan kudade don a zabe su.

Da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis yayin kaddamar da wani littafi mai taken “Siyasar jam’iyyu” wanda Dokta Mohammed Wakil ya wallafa, Jonathan ya ce abin kunya ne yadda ’yan takara ke biyan kudi sannan su bukaci a dawo musu da su idan suka sha kaye a zabukan.

Jonathan ya ce, “Gaba daya yadda zabukan fid da gwani ke gudana a kasar nan abin takaici ne. Tsarin ya sami matsala.

“Bai kamata a ce muna amfani da wannan tsarin wajen zabar Shugaban Kasa da Gwamnoni da ’yan majalisun tarayya da na jihohi ba.

“Tsarin ya fadi warwas, kuma bai dace da Najeriya ba, amma haka za mu ci gaba da maleji da shi.

“Muna addu’ar Allah ya ba mu shugabanni na gari, amma abin da ya faru a 2022 muna fatan kada ya sake faruwa a kasar nan,” inji tsohon Shugaban.

Daga nan sai Jonathan ya bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta yi dokokin da za su haramta bayar da kudade ga daliget da sauran masu zabe.

Ko a makon nan Aminiya ta rawaito yadda dan Namadi Sambo, wanda shi ne Mataimakin Jonathan zamanin yana Shugaban Kasa ya nemi daliget su dawo masa da kudaden da ya kashe musu bayan ya fadi a zaben.