✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mutu bayan lalata da matar aure a otel

Budurwarsa, wadda matar aure ce a unguwar, ta sume jim kaɗan bayan mutuwarsa

Wani magidanci ya yanke jiki ya mutu bayan sun gama lalata da budurwarsa a dakin otel.

Bayan sun gama saduwa ne magidancin mai ’ya’ya biyu, ya mutu a otel din da ke unguwar Akinjagunla a Jihar Ondo.

Ganin haka ne budurwa tasa, wadda matar aure ce a unguwar, ta fara ihun neman agaji, inda kafin a zo ta yanke jiki ta fadi a sume, amma aka farfaɗo da ita.

Shaidu sun bayyana wa wakilinmu cewa an kai gawar mamacin wanda ma’aikacin gwamnati ne Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kimiyya da ke garin Ondo.

Wani shaida da wakilinmu ya tattauna da shi ya yi zargin kulumboton da mijin matar ya yi ne ya kama ta da kwarton nata.

“Ita ce ta yi kururuwa bayan kwarton nata ya yanke jiki ya fadi, manajan Obele din da sauran mutane sun garzaya domin su ceto shi, amma daga bisani aka tabbatar cewa ya rasu,” in ji shi.

Ya ce daga baya hukumar gudanarwar otel din ta sanar da babban ofishin ’yan sanda da ke Yaba, kafin a kai gawar asibiti.

Kakakin ’yan sandan jihar, Fumilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da aukuwar lamarin da kuma tsare wasu mutum biyu da ake zargi domin gudanar da bincike.