✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya zama dole Buhari ya bar batun kirkiro sabbin ma’aikatu’

Rahoton kwamitin gyaran ma'aikatun Gwamnatin Tarayya ya taka wa Buhari burki kan kirkiro sabbin hukumomi ko ma'aikatu

Kwamitin yi wa hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya gyaran fuska domin rage kashe kudade ya bukaci gwamnatin ta dakatar da kirkiro sabbin hukumomi ko ma’aikatu a halin yanzu.

Shugabannin kwamitin da suka hada da tsoffin Shugabannin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Steve Orosanye, Amma Pepple da Oladapo Afolabi, sun bayyana haka ne a yayin da suke mika rahotonsu ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ranar Talata.

Rahoton kwamitin ya ce, “Wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kafa sabbin hukumomi ko ma’aikatu, saboda babban aikin da ta sa wannan kwamiti shi ne rage kashe kudaden gudanar da gwamnati.”

Amma Pepple ta ce, rahoton ya kuma bukaci Hukumar Tsara Albashi ta Kasa ta tsaya a kan aikinta, ta daina sahale biyan albashi da alawus din masu rike da mukaman siyasa, sannan ta hana su nada masu taimaka musu yadda suka ga dama.

Ta kuma bayyana cewa rahoton nasu ya bayar da shawarwarin ne daidai da aikin da aka ba su na rage kashe kudaden tafiyar da gwamnati da kuma hana cuwa-cuwa da shiga aikin juna gami da tabbatar da kwarewa a aikin gwamnati

Sai dai kuma ta bayyana damuwar kwamitin cewa karba da kuma yiwuwar aiwatar da rahoton nasu na zuwa ne a gab da zaben 2023.

Ta ce duk da haka, Najeriya ta dade tana bukatar rage almubazzaranci wajen gudanar da gwamnati domin samun kudaden da za ta kyautata rayuwar al’ummar kasar.

“Yin hakan na da matukar muhimmanci, saboda idan aka lura, daga kasafin kudin 2022 za a kashe Naira tiriliyan 5.47 (kashi 39 cikin 1oo) na kudaden ne a kan hukumomi da ma’aikatun gwamnati da kuma biyan basuka.

“Muna fata Gwamnatin Tarayya za ta kammala nazarin rahoton a kan lokaci sannan ta fara aiwatar da shi domin amfanin jama’ar Najeriya.”

Da yake karbar rohoton, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ba wa kwamitin tabbacin cewa a shirye Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake ya bayar da goyon baya tare da aiwatar da sauye-sauyen da suka dace a bangarorin tattalin arzikin Najeriya.