✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka cafke barayin karfen titin jirgin kasa a Neja

An ritsa su sun makare manyan motocin uku da karfunan titin jirgin kasa

’Yan sanda sun kama mutum 21 da karafunan titin jirgin kasa da ake zargin sun sato ne domin sayarwa a Jihar Neja.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta ce ta damke mutanen ne bayan samun rahoton aikace-aikacen mutanen a unguwar Esheti-Elegi da ke Kataeregi,  Karamar Hukumar Katcha ta Jihar.

Yayin gabatar da wadnda ake zargin a hedikwatar Rundunar da ke Minna, kakakin Rundunar, DSP Wasiu A. Abiodun, ya ce jami’ansu da ke sintiri ne suka yi nasarar kama 17 daga cikin mutum 21 a ranar Laraba.

Ya ce bayan samun labari, ’yan sanda sun ritsa mutanen sun makare wasu motocin kanta uku da karfunan titin jirgin kasa da suka kwakkwance da wadanda suka yanke za su tafi da su.

Abiodun ya ce an kuma kame motocin da direbobinsu tare da mutanen a lokacin, daga baya aka kamo shugaban gungun, wanda ya ce wani babban dan gwangwan ne ya ba su kwangilar samo masa karafunan layin dogo.

Ko a ranar 17 ga watan Maris, Rundunar ta kama wasu mutum biyu da motocin kanta makarare da karafuna 80 na cikon titin jirgin kasa a kan babbar hanyar Kataeregi zuwa Minna.

Kakakin Rundunar ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin kafin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Minna.