✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Aka Harbe Wata Mata A Filin Idi A Gusau

Ana zargin jami’an tsaron sun biyo wasu ɓata-gari ne suna harbi da bindiga har aka yi kuskuren samun matar.

Mazauna birnin Gusau da ke Jihar Zamfara sun shiga ruɗani bayan an harbi wata mata da ta fito sallah a masallacin Idi. 

Ana zargin jami’an Hukumar Sibil Difens da harbin matar da ba ta ji ba ba ta gani ba yayin gudanar da Sallar Idin da aka yi ranar Laraba da ta gabata.

An bayyana cewa jami’an sun biyo wasu ɓata-gari ne suna harbi da bindiga har aka yi kuskuren samun matar.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa lamarin ya fusata mutane, dalili ke nan da suka afka wa jami’an hukumar tsaron, har suka kone musu motar da suke sintiri da ita a yankin.

Kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, tuni aka kama jami’an tsaron guda biyu da ake zargi da aikata kuskuren.

“Yanzu haka mutum biyu da ake zargi da harbin na tsare a wurinmu. Hukumarsu ta Sibil Difens kuma suna bincike kan gaskiyar abin da ya faru.”

A nasu ɓangaren, kakakin rundunar Sibil Difens a Jihar Zamfara ya ce, “Abin da ya faru shi ne, mun girke jami’an mu a shataletaletalen Bankin UBA, to daga can ne suka ji harbin bindiga sai suka kai ɗauki. A can suka samu matar da aka harba da bindiga.”